'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 17 yayin harin Sokoto, Ɗan Majalisa
- Aminu Gobir, Dan majalisar jihar Sokoto ya tabbatar da rasuwar jami'an tsaro 17 yayin harin Sokoto
- A cewar dan majalisar, wadanda suka rasu sun hada da soji 9, 'yan sandan biyar da jami'an NSCDC uku
- Wata majiya da rundunar 'yan sandan jiha Sokoto ta tabbatar da harin tana mai cewa an kai gawarwakin Asibitin Kwararru na Sokoto
Dan majalisar jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Gobir, ya ce an kashe jami'n tsaro 17 yayin harin da aka kai kauyen Dama a jihar, Premium Times ta ruwaito.
Premium Times ta ruwaito cewa an kashe sojoji da dama yayin da wasu suka tsere sakamakon harin da aka kai musu a sansaninsu da ke wani makaranta a kauyen.
'Yan ta'addan sun kone wani motar jami'an tsaron yayin harin.
Mista Gobir ya ce jami'an tsaron da aka kashe akwai sojoji tara, yan sanda guda biyar da kuma jami'an hukumar tsaro ta NSCDC guda uku.
Dan majalisar ya kara da cewa akwai jami'an tsaron da ba a gano inda suke ba tun bayan harin na ranar Juma'a.
Abokin daya daga cikin jami'an NSCDC da suka kwanta dama ya tabbatar da rasuwarsa
Wani abokin daya daga cikin jami'in NSCDC da aka kashe yayin harin, Rilwanu Nagwaria, ya ce jami'in mai suna Sulaiman ya mutu a matsayin jarumi.
Mr Nagwaria ya ce:
"Ya rasa ransa, ya mutu domin kare hakkin wasu ... mu tuna cewa 'yanci na da wuyan samu kuma mu rika wadanda suka sadaukar da rayyuwansu don mu samu 'yancin."
Wata majiyar tsaro daga rundunar yan sandan jihar Sokoto ta ce an kai gawarwakin su zuwa Asibitin Kwararru na Sokoto.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu
A wani labarin daban, 'yan bindiga, a ranar Alhamis, da yamma sun kai hari garin Shinkafi, inda har suka kutsa ofisoshin 'yan sanda suna ta harbe-harbe yayin harin kamar yadda Daily Trust Saturday ta ruwaito.
Rahoton ya ce maharan sun sace bindigu da dama yayin da suka kai harin ofishin 'yan sandan.
Kawo yanzu ba a kammala samun cikaken bayani ba, duba da cewa Shinkafi na cikin garuruwan da aka datse wayar tarho sun farkon wannan watan kamar yadda jami'an tsaro suka bukata.
Asali: Legit.ng