Majalisar dokoki ta tsaurara matakan tsaro kan wata zanga-zangar ma'aikata

Majalisar dokoki ta tsaurara matakan tsaro kan wata zanga-zangar ma'aikata

  • Ma'aikata a majalisar dokoki sun fusata, sun shirya zanga-zanga don neman hakkinsu na albashi
  • Majalisar dokoki ta tsaurara tsaro a harabar majalisa bisa tsoron abin da ka iya biyo bayan zanga-zanga
  • Ma'aikatan sun koka kan yadda suke bin bashi mai yawa daga gwamnati, wannan ya dauki tsawon shekaru

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar na nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar Dokoki ta kasa domin dakile wata zanga-zangar da wasu masu taimaka wa majalisar suka shirya.

Majalisar a safiyar ranar Litinin, Litinin, 27 ga watan Satumba, ta tsaurara matakan tsaro bayan ma’aikata karkashin kulawar ma’aikatan majalissar suka tunzura don gudanar da zanga-zanga kan batun albashinsu.

Da Duminsa: Majalisar dokoki ta tsaurara matakan tsaro bisa tasowar zanga-zanga
Majalisar dattawa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jami'an tsaro da suka hada da masu kwantar da tarzoma da 'yan sanda na yau da kullum, ma'aikatan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami'an tsaron majalisa duk hallara don kula da hanyoyin shiga da fita daban-daban a harabar majalisar.

Kara karanta wannan

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

An kuma lura cewa ba a rufe kofofin da ke kaiwa dakin shiga fadar White House daga dakunan majalisar dattawa da na wakilai ba amma jami'an tsaro na gadinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Musabbabin wannan zanga-zangar

Ku tuna cewa mataimakan 'yan majalisun dokokin Najeriya sun kudurta dakatar da ayyukan majalisar daga ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, sakamakon rashin biyansu albashi da alawus-alawus na naira biliyan 3.1, inji rahoton PM News.

Ma’aikatan majalisar suna ikirarin cewa babban bashin ya samo asali ne daga bashin albashi na naira biliyan 1.35 da kuma biliyan N1.75 na kari da aka yi na mafi karancin albashi.

Mataimakan sun kara da cewa yayin da har yanzu mataimaka 1,300 ke bin bashin albashi, ko da daya daga cikin ma’aikatan 2, 345 a NASS bai sami karin da aka yi na mafi karancin albashi ba tun watan Yunin 2019.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ganduje ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim, sabon Sarkin Gaya

Abin kunya ne Najeriya ta ke kiran kanta uwa ga Afrika, inji tsohon sarkin Kano Sanusi II

A wani labarin, Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya ce Najeriya ta rasa kimarta a matsayin uwa a Afirka ga sauran kasashen da suka bunkasa tattalin arzikin su, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanusi ya ce yanzu Najeriya tana bayan sauran wasu kasashen Afirka da yawa idan aka duba ta fuskar ci gaba.

Sanusi wanda ya kasance Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya fadi haka ne a yayin rufe taron Babban Taron Zuba hannun Jari na Kaduna, mai taken, ‘KadInvest 6.0.’

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.