Gwamnatin Amurka ta tattara shaidu 6,700 don tabbatar da laifin Abba Kyari
- Yayin da ake ci gaba da jiran bayanai kan batun shari'ar Abba Kyari, Amurka ta shirya bayanai da hujjoji
- A bangaren hujjojin da za a gabatar, Amurka ta shirya wasu shaidun da suka kai 6,700 kan Abba Kyari
- Hushpuppi ya amsa laifinsa, abin da yake jira a yanzu shine hukunci yayin da ake ci gaba da binciken Abba Kyari
Rahoton da Premium Times ta fitar ya nuna gwamnatin Amurka ta tattara fiye da fayilolin na'ura 2,700 a wani bangare na shaidun da za a gabatar a shari’ar zambar dala miliyan 1.1 da ta shafi wani babban jami’in ‘yan sandan Najeriya, Abba Kyari.
Jaridar ta ambaci takaddar kotu wacce ta ce tana kuma nuna wasu jerin rahotannin bincike da “sabbin abubuwan da aka gano” gami da takaddun da aka samo daga hukumomin tilasta bin doka da ke da shafuka sama da 6,700 wadanda masu gabatar da kara suka nuna.
An tattaro cewa bangaren Kyari da na Amurka sun shigar da bukatar dage karar a ranar Juma'a, 24 ga watan Satumba, bisa dalilai daban-daban.
An samu rahoton cewa lauyoyin da ke kare Kyari sun nemi karin lokaci don shiryawa shari'ar yayin da masu gabatar da kara a bangaren Amurka ma suka nemi karin lokaci don gabatar da tarin takardu, ciki har da wadanda aka samu daga kasashen waje.
Dangane da bukatun, gwamnatin Amurka ta riga ta ba lauyoyin da ke kare Kyari kusan 2.31GB na bayanai da suka kunshi fayilolin na'ura 2,707.
Fayilolin sun kunshi, hirar Kyari na waya wanda aka fi sani da 'chats', rahoton Cellebrite, sakwannin WhatsApp, nadadden sauti, da sauran bayanai na kafofin watsa sada zumunta, in ji rahoton.
Rahoton ya kara da cewa masu gabatar da kara suna tattara kusan shafuka 6,773 na karin binciken da ake tsammanin za a samar cikin makwanni biyu.
Legit.ng ta tattaro cewa uku daga cikin wadanda ake kara kan batun, Rukayat Fashola (Morayo), Bolatito Agbabiaka (Bolamide), da Yusuf Anifowoshe (AJ da Alvin Johnson) a shirye suke don a gurfanar da su.
Mutanen uku da aka kama a Amurka kuma daga baya aka sake su bisa beli sun sanya hannu kan bukatar a dage shari'ar su zuwa watan Mayun 2022 tare da gabatar da lauyoyin su daban da masu shigar da kara na Amurka.
Sai dai, sauran wadanda ake tuhuma uku da ake zargi suna waje da Amurka wadanda suka hada da Kyari, Abdulrahman Juma, da Kelly Chibuzo Vincent, a cewar masu shigar da kara na Amurka.
Duk wadanda ake tuhuma shida ciki har da Kyari, sun hada kai ne a cikin wata damfarar $1.1m da shahararren dan Instagram na Najeriya, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi ya shirya.
Dangane da takaddun da cibiyar FBI ta fitar, an ce wani dan kasuwa na kasar Qatar ya kasance wanda aka so cuta a karkashin jagorancin Hushpuppi tsakanin Nuwamba 2019 da Afrilu 2020.
A halin da ake ciki, Hushpuppi ya amsa laifuka daban-daban na zamba ciki har da shirin zambar $1.1m a wata shari’ar da ke gaban kotun gundumar Amurka da ke tsakiyar California. Yanzu yana jiran hukunci.
Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari
A wani labarin, Hadin gwiwar Kungiyoyin Arewa sun yi zargin cewa cibiyar bincike ta FBI da rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) sun take hakkin Abba Kyari kai tsaye na bincikensa da ake.
A cewar kungiyar, Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP), ba a ba shi damar yin bayani ba kawai FBI da NPF suka dauki matakin gaggawa a kansa.
Don haka, sun nemi a gaggauta duba dakatarwar Kyari sannan a mika shari'arsa ga Hukumar Leken Asiri ta Najeriya.
Asali: Legit.ng