Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas Yana Daf Da Durƙushewa, NPYA Ta Yi Gargaɗi

Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas Yana Daf Da Durƙushewa, NPYA Ta Yi Gargaɗi

  • Wata kungiyar matasa masu muradin kare al'ummar Arewa-maso-gabas ta yi gargadin cewa tattalin arzikin yankin na daf da durkushewa
  • Kungiyar ta bada shawarar cewa ya kamata gwamnonin arewa su hada kudi domin kafa wata banki na yankin a maimakon dogaro da na kudu
  • A cewar kungiyar, kiraye-kirayen da gwamnonin kudu ke yi na ba basu damar su rika karbar harajinsu ya isa zama darasi ga gwamnonin yankin

Wata kungiyar matasan arewa idan har jihohin Arewa-maso-gabas, NPYA, ta ce ya zama dole jihohin yankin su rubanya harajin da suke samu, su kuma kafa banki domin tallafawa yankin idan ana son kawo karshen talauci, rashin aiki da matsalar tsaro, The Sun ta ruwaito.

Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas Yana Daf Da Durƙushewa, NPYA Ta Yi Gargaɗi
Taswirar Yankunan Nigeria. Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Kungiyar cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Sabiu Tirzimi, ta bada shawarar jihohin Arewa-maso-gabas su bude wani asusu don zuba Naira biliyan biyar-biyar, da za a iya assasa babban bankin kasuwanci na bai-daya.

Kara karanta wannan

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

NPYA ta yi kira a yi koyi darasi daga Gwamnan Bauchi

A kan bukatar gwamnonin na kudu maso gabas su habaka hanyoyin kudin shiga, kungiyar ta yi kira ga gwamnonin su yi koyi da irin tsare-tsaren da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi yake aiwatarwa wajen tattara haraji da ke bashi daman yi wa jama'arsa aiki.

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa gwamnatocin tarayya da suka gabata sun gaza cika wa yankin alkawurra da suka dauka, musamman na aikin Wutar Mambila wanda ya yanzu ya zama labarin kanzon kurege.

Sanarwar ta bayyana cewa muddin gwamnonin ba su yi hakan ba, to sauran bankunan kasuwanci guda 30, na 'yan kudancin kasar nan za su ci gaba da mamaye ko'ina a yankin, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na APC saboda dokar hana kiwo a fili

A cewar kungiyar:

"Kiraye-kirayen da gwamnonin yankin kudu ke yi a kafafen watsa labarai kan neman a basu damar karbar harajinsu ya kamata ya zama darasi ga gwamnonin arewa su habaka hanyoyin samun kudin shiga ko kuma su fada matsala na dogaro da gwamnatin tarayya."

VAT: Arewa na da arziki, Za mu iya rayuwa ba tare da dogaro da kudu ba, Hakeem Baba-Ahmed

A wani labarin daban, Kakakin kungiyar dattawan arewa, NEF, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce arewa za ta iya ci gaba da rayuwa ko babu taimakon jihohin kudancin Najeriya.

An samu cece-kuce iri-iri akan yadda jihar Ribas da Legas suka sanya dokar rike kudaden harajin su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kotun daukaka kara ta umarci jihohin akan kada su amshi kudaden harajin amma gwamnatin jihar Ribas ta daukaka kara zuwa kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel