Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na APC saboda dokar hana kiwo a fili

Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na APC saboda dokar hana kiwo a fili

  • Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na Najeriya kan dokar hana kiwo a fili a yankin kudu
  • Wannan ya biyo bayan yadda jihohin kudu ke haba-haban sanya doka kan makiyaya a yankunansu
  • Gwamna El-Rufai ya ce hakan ba daidai bane, shi kuwa gwamnan Akeredolu ya zargi El-Rufai da tsallafawa barna

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya caccaki takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, kan kalaman da ya yi game da dokar hana kiwo a fili.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Gwamna El-Rufai ya bayyana dokar hana kiwo a fili da wasu daga cikin gwamnonin kudu ke sanyawa a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Sai dai Gwamna Akeredolu a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Donald Ojogo ya fitar, ya ce bai kamata irin wannan magana ta fito daga shugaba ba, inji jaridar.

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

Rikici ya barke tsakanin gwamnoni saboda dokar hana kiwo a fili
Makiyaya a kan hanya | Hoto: rfi.fr
Asali: UGC

Gwamna Akeredolu wanda yake jam’iyya daya da El-Rufai; jam’iyyar APC, ya zargi gwamnan na Kaduna da yin iya bakin kokarinsa wajen kai ‘yan ta’adda zuwa yankin kudanci a karkashin wani ra’ayinsa da ke kare aikata barna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da alamu El-Rufai na kulla makircin tura 'yan ta'adda yankin kudanci, Akeredolu

Ya ce kalaman na Gwamna El-Rufai "kawai yana neman karfafa tashin hankali ne a karkashin fushin doka daga masu ruwa da tsaki da abin ya shafa."

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Gwamna Akeredolu ya ce duba da tsokacin na El-Rufa'i da alamu yana kulla makirce-makircen kai 'yan bindiga yankinsu.

Jaridar ta bayyana cewa Gwamna El-Rufai ya zargi gwamnonin kudu da siyasantar da rikicin manoma da makiyaya tare da kafa dokar hana kiwo a fili.

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata

A wani labarin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi gargadin a kula game da komawar 'yan bindigan da yunwa ta fatattaka, zuwa garuruwa da yankuna don satar kayayyakin gona kafin lokacin girbi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnan ya yi gargadin ne a ranar Talata 21 ga watan Satumba, a Katsina, a wani taron shawari da ya yi da Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed kan yanayin tsaro a jihar.

Taron ya samu halartar Shugabannin hukumomin tsaro na jihar, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.