VAT: Arewa na da arziki, Za mu iya rayuwa ba tare da dogaro da kudu ba, Hakeem Baba-Ahmed

VAT: Arewa na da arziki, Za mu iya rayuwa ba tare da dogaro da kudu ba, Hakeem Baba-Ahmed

  • Kakakin dattawan arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce arewa tana da arzikin da za ta tsayu da kan ta ba tare da ta dogara da jihohin kudu ba
  • An dinga cece-kuce tun bayan jihar Rivers da Legas su ka sanya dokar karbe harajin su, duk dai kotun daukaka kara ta hana su hakan
  • A wata tattaunawa da gidan talabijin din Arise su ka yi da Baba-Ahmed, ya bayyana cewa dama arzikin arewa ya isheta ba tare da taimakon kudu ba

Jihar Kaduna - Kakakin kungiyar dattawan arewa, NEF, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce arewa za ta iya ci gaba da rayuwa ko babu taimakon jihohin kudancin Najeriya.

An samu cece-kuce iri-iri akan yadda jihar Ribas da Legas suka sanya dokar rike kudaden harajin su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

VAT: Arewa na da arziki, Za mu iya rayuwa ba tare da dogaro da kudu ba, Hakeem Baba-Ahmed
Kakakin NEF, Dr Hakeem Baba-Ahmed. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun daukaka kara ta umarci jihohin akan kada su amshi kudaden harajin amma gwamnatin jihar Ribas ta daukaka kara zuwa kotun koli.

Dama arewa tana da arzikin ta cewar Baba-Ahmed

A wani shiri na Arise TV a ranar Talata, Baba-Ahmed ya ce arewa tana da arziki kuma bata bukatar taimakon wani yanki.

Bisa ruwayar Daily Trust, Baba-Ahmed ya kada baki ya ce:

“Zan bayar da shawarar mu tsaya mu ji hukuncin da kotu za ta yanke. Duk da haka ya kamata a gyara yadda ake tafiyar da ayyukan kasar nan.
“Mun dade muna bin bayan sauya tsare-tsare da gyara a arewa. Mun bukaci wata kungiya ko kuma majalisar tarayya ta yi magana akan irin wannan lamarin.
“Idan ba mu yi hakan ba a yanzu, mu nemi shugaban da zai yi hakan a 2023. Ya kamata wannan mulkin ya fahimci muhimmancin sauya tsari da gyare-gyare. Sannan mu ‘yan arewa mu gane cewa ya kamata mu canja hanyar samun kudaden shiga.

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

“Maganar gaskiya arewa tana bukatar gyara. Mu yanki ne masu arziki kuma zamu iya ci gaba da abinda muke da shi ba tare da dogaro da sauran jihohi ba. Talaucin mu ba irin wanda zai iya janyo a raba kasar nan bane.
“A arewa muna da mutane da dama da suke bukatar ci gaba, babbar matsalar mu shine muna da mutane masu yawan gaske da har yanzu basu ci gaba ba. Ya kamata mu bunkasa mutanen yankin mu.
“Muna bukatar shugabanni masu fahimta, gwamnatin yanzu bata fahimci hakan ba. Idan banda hakan da ta zura wa kotu ido ta yanke hukunci.
"Noma shine babban tushen arziki, muna da ruwa, dabbobi da ma’adanai da suke bukatar a hako su amma gwamnonin mu ba su fahimci hakan ba. Kuma hakan ba daidai bane.”

Dangane da zaben 2023

Akan batun zaben 2023, Baba Ahmed ya ce babu bukatar gwamnonin kudu basu gabatar da bukatar samar da shugaban kasa a cikin su yadda ya dace ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

Kamar yadda ya ce:

“Babu wani abu dangane da arewa da ke nuna tana yi wa shugabancin ‘yan kudu zagon-kasa. Mun fahimci masu cewa indai ana son wanzuwar adalci da zaman lafiya wajibi ne a kawo ‘yan kudu don su shugabanci kasa. Ba haka ake yi ba idan ana bukatar mulki.
“Ba zaku tsorata mu da rikici ba. Zamu iya duba kundin tsarin mulki, anan zamu gane abubuwan da ake nema idan mutum zai zama shugaban kasa. Wajibi ne ya samu akalla kashi 25 bisa dari na jihohi 24. Wanda hakan yake nuna cewa babu dan arewan da zai iya zama shugaban kasa har sai ya samu goyon baya daga kudancin Najeriya."

Gwamna Sule: Dokar hana kiwo da wasu jihohi suka saka bata aiki

A wani labarin daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce dokar hana kiwo a fili da wasu takwarorinsa suka saka a jihohinsu baya aiki.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe

Gwamnoni jihohin Enugu, Rivers, Akwa Ibom, Ondo da Legas duk sun rattaba hannu kan dokar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnonin jihohin na Kudu sun tsayar da ranar 1 ga watan Satumban 2021 a matsayin ranar da za a rattaba hannu kan dokar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel