Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

  • Nasir El-Rufa'i ya bayyana abinda gwamnonin Arewa ke yi kan lamarin kiwo a fili
  • Gwamnan ya bayyana cewa kudi suke bukata don yankan filaye na musamman ga Fulani Makiyaya
  • Ya yi martani kan dokokin da gwamnonin kudancin Najeriya ke kafawa na haramta kiwo a fili

Abuja - Gwamnan jihar Kaduna ya caccaki gwamnonin kudancin Najeriya kan sabuwar dokar haramta kiwo a fili da suke yi a jihohinsu.

El-Rufa'i a martaninsa kan wannan doka, ya ce ba kafa dokar bane abu mai muhimmanci, aiwatar da dokar ne ba zai yiwu ba.

Zaku tuna cewa kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, sun yi ittifakin kafa dokar a yankinsu.

Jihohi irinsu Ondo, Oyo, Lagos, Enugu, Osun, Akwa Ibom da sauransu tuni sun kafa dokar.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na APC saboda dokar hana kiwo a fili

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu
Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma yayin hira da manema labarai ranar Talata a hedkwatar All progressives Congress (APC) dake Abuja, El-Rufa'i yace duk da cewa akwai bukatar makiyaya su daina yawo da dabbobi kamar yadda suka saba, mafita ba shi bane kafa dokokin da ba za'a iya aiwatarwa ba, rahoton Leadership.

Ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun yi ittifakin cewa mafita shine tsarin kiwo a gida kuma gwamnatin ta shirya filayen kiwo a Kaduna da makiyaya 1500 zasu iya kiwo a wajen tare da iyalansa.

Yace:

"Kungiyar Gwamnonin Arewa ta dauki matsayin cewa kiwo a fili ba shi bane hanya mafi dacewa da kiwo ba. Kuma wajibi ne mu koma kiwo a gida."
"Muna da shiri, sai mun samuu dukiya kuma zamu iya aiwatarwa yadda ya kamata. Ba magana kafa doka yau ko gobe bane, wannan ba shi bane mafita."

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

"Shirmen da ake yi shine siyasantar da abun da kuma kafa dokoki da kuka san cewa ba zai yiwu a aiwatar ba."

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya caccaki Nasir El-Rufai kan kalamansa

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya caccaki takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, kan kalaman da ya yi game da dokar hana kiwo a fili.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Gwamna El-Rufai ya bayyana dokar hana kiwo a fili da wasu daga cikin gwamnonin kudu ke sanyawa a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Sai dai Gwamna Akeredolu a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Donald Ojogo ya fitar, ya ce bai kamata irin wannan magana ta fito daga shugaba ba, inji jaridar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel