Buhari ga shugabannin duniya: Mun nakasa Boko Haram, kananan wurare su ke kai farmaki yanzu

Buhari ga shugabannin duniya: Mun nakasa Boko Haram, kananan wurare su ke kai farmaki yanzu

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk da rusa kungiyar Boko Haram har yanzu ta na nan ta na aika-aika ta karkashin kasa
  • A cewar sa, duk da kokarin sojoji wurin ragargazar su har yanzu suna ci gaba da ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya
  • Shugaban kasa ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taro na majalisar dinkin duniya da aka yi a birnin New York da ke Amurka

New York - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an raba kan mayakan Boko Haram kuma an rusa su.

TheCable ta ruwaito cewa, a cewar sa, duk da kokarin sojoji wurin ragargazar su har yanzu suna ta’addancin su kuma ba su daina kai farmaki ba.

Kara karanta wannan

Shehun Borno ya amince da dawo da tubabbun 'yan Boko Haram cikin jama'a da suka yi wa ta'addanci a baya

Buhari ga shugabannin duniya: Mun nakasa Boko Haram, kananan wurare su ke kai farmaki yanzu
Buhari ga shugabannin duniya: Mun nakasa Boko Haram, kananan wurare su ke kai farmaki yanzu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya yi wannan furucin ne a ranar Juma’a a wani taron majalisar dinkin duniya a birnin New York dake Amurka.

A cewar sa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ta’addanci na ci gaba da yaduwa a fadin duniya. A Najeriya, duk da sojoji sun raba kan kungiyar Boko Haram kuma an rusa ta, ta na ci gaba da kai wa jama’a farmaki. Najeriya za ta ci gaba da yin aiki tukuru da UN wurin ganin an kawo karshen ta’addanci a kasar.
“Najeriya ta yi iyakar kokarin ganin ta kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya da yankin tafkin Chadi, da kuma ‘yan bindiga da suke addabar arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
“Jami’an tsaron Najeriya sun samu nasarori masu tarin yawa yayin yaki da ta’addanci. Sakamakon kaimin da sojoji suka kara, mayaka da dama sun zubar da makamansu.”

Kara karanta wannan

Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai

Shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta yi iyakar kokarin ganin ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mata, yara, masu nakasa, ‘yan gudun hijira da sauran su.

Ya yi kira ga duniya a kan a taru a kawo karshen cin zarafin da ake yi wa mata da yara, TheCable ta wallafa.

Shugaban kasa ya kara da kira a kan tsanar da ke karuwa a fadin duniya na banbancin launin fata da sauran su tsakanin jama’a.

Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa

A wani labari na daban, kwamandan rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai, Maj.-Gen. Christopher Musa, ya ce dakarun sojin Najeriya ba za su bar kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta samu wuri tare da yin kane-kane a Najeriya ba.

Musa ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Kamar yadda ya ce, ISWAP kungiyar ta'addanci ce ta ketare wacce wasu daga kasashen ketaren ke daukar nauyin ta, ta yuwu kuma akwai wasu 'yan Najeriya da ke daukar nauyin ta. Don haka ba ta da wurin zama a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng