Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai

Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai

  • A ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba da safe aka samu labarin mutuwar Dr Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin shugaban CBN, mutuwar da ta girgiza zukata da dama
  • Ya rasu yana da shekaru 64 bayan wata kwarya-kwaryar jinya da ya yi a asibitin koyarwa na Abuja da ke Gwagwalada, wanda yau kwana 5 kenan
  • Mutane da dama sun yi ta cece-kuce akan yadda Buhari da El-Rufai har yau ba su tura sakon ta’aziyyar su ba duk da yadda ake tururuwar yin hakan

Jihar Kaduna - Idan kasa ta rufe idon mamaci, mutane za su ga abubuwan mamaki, wannan maganar ta yi kama da labarin tsohon mataimakin babban bankin Najeriya, CBN, Dr Obadiah Mailafia wanda ya rasu da safiyar Lahadi, 19 ga watan Satumban 2021.

Mailafia ya mutu ya na da shekaru 64 a asibitin koyarwa na jami’ar Abuja da ke Gwagwalada bayan wata kwarya-kwaryar jinya da ya yi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai
Marigayi Dr Obadiah Mailafia. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Mutuwar sa ta girgiza zukata da dama

Mutuwar sa ta girgiza ‘yan Najeriya da dama wanda kowa ya san yadda ya taimaka ta hanyar yi wa kasa bauta a harkar tattalin arziki.

Manyan kungiyoyi irin kungiyar gwamnonin arewa, kungiyar kiristoci ta arewa, kungiyar mutanen kudancin Kaduna da sauran su sun mika sakon ta’aziyyar su.

Saidai kamar yadda aka saba shugaban kasa yana tura ta’aziyya kamar yadda ya yi ga mawaki Sunday Adegeye wanda aka fi sani da Sunny Ade na mutuwar matar sa, Risikat Adegeye, har yau kwana 5 kenan da mutuwar Mailafia babu wata takardar ta’aziyya daga fadar shugaban kasa.

Shugaban kasa ya tura ta’aziyyoyin mutuwa da aka yi bayan mutuwar Mailafia

The Punch ta ruwaito yadda fadar shugaban kasa ta bayyana alhini akan mutuwar sarkin Gaya, Ibrahim Abdulkadir, wanda ya rasu ranar Laraba, 22 ga watan Satumba bayan kwana 4 dda rasuwar Mailafia.

Har ila yau fadar ta taya firayim ministan Canada, Justin Trudeau murnar samun nasarar cin zabe a ranar 21 ga watan Satumba.

Haka zalika gwamnatin jihar Kaduna a matsayin jihar sa ba ta tura sakon ta’aziyyar ta ba dangane da mutuwar Mailafia saidai har gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya tura nasa sakon inda ya ce Mailafia mai kishin kasa ne.

The Punch ta yi kokarin ganin ta tattauna da kakakin shugaba, Femi Adesina don jin ta bakin sa ta hanyar kiran sa a waya amma be dauka ba kuma bai bayar da amsar sakon da wakilin Punch ya tura ma sa ba.

Har ila yau, The Punch ta yi kokarin tattaunawa da Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed da kakakin sa , Segun Adeyemi duk ba a samu nasara ba kuma ba su bayar da amsar sakon da aka tura musu ba.

Sannan har neman hadimin gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye anyi, bai dauki waya ba kuma bai bayar da amsar sakon da wakilin The Punch ya tura masa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel