Shehun Borno ya amince da dawo da tubabbun 'yan Boko Haram cikin jama'a da suka yi wa ta'addanci a baya

Shehun Borno ya amince da dawo da tubabbun 'yan Boko Haram cikin jama'a da suka yi wa ta'addanci a baya

  • Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi a ranar Laraba ya ce yanzu haka ana kokarin dawo da tubabbun ‘yan Boko Haram cikin mutane
  • A cewar shugaban za a mayar dasu ne don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma inda ya ce tubabban ‘yan ta’addan sun gane kuskuren su
  • Ya bayyana hakan ne yayin wani taro na kaddamar da kamfen din wayar da jama’a akan shirye-shiryen mayar da tubabbun mayakan cikin jama’a a Maiduguri

Jihar Borno - Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi a ranar Laraba ya ce ana ta kokarin ganin an kammala shirin mayar da tubabbun mayakan Boko Haram cikin jama’a don samar da zaman lafiya mai dorewa cikin al’umma.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, shugaban gargajiyan ya yi maganar ne a wani taro na kamfen din wayar da kai wurin kokarin mayar da tubabbun mayakan cikin jihar Maiduguri.

Kara karanta wannan

FG ta gano kuma ta taka wa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya birki, Malami

Shehun Borno ya amince da dawo da tubabbun 'yan Boko Haram cikin jama'a da suka yi wa ta'addanci a baya
Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa ta’addanci a jihar ya dauki lokaci mai tsawo kuma mutanen jihar a shirye suke da a hada kan su da su don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A cewar sa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito,

tubabbun mayakan sun gane kuskuren su kuma a shirye suke da su cigaba da harkoki da jama’an gari.

Kamar yadda ya ce:

“Batun Boko Haram abu ne sananne a wurin mu kuma muna ta kokarin ganin kawo karshen wannan lamarin tsawon lokaci. Da za a kawo karshen shi gaskiya da kowa ya ji dadi.”
“Kamar yadda kowa ya sani, shugabannin gargajiya ciki har da dagacin kauyuka da malaman addini duk sun yarda da maganar mayar da su cikin jama’an gari.”

El-Kanemi ya ce kowa ya bai wa shugabanni hadin kai

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Shugaban ya roki jami’an gari da su taru su yi aiki da shugabannin kananun hukumomi, gundumomi da shugabannin kauyaku wurin kawo zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan harkokin cikin gida, labarai da al’adu, Alhaji Babakura Abba Joto, ya ce yanzu haka mayakan da suka tuba sun kai 6,000 sai dai ba za a mayar dasu cikin jama’a ba har sai an gama tantance su an gyara su tukunna.

Kwamishinan harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo, ta ce matan da suka mika wuya da dama sun shiga ta’addancin ne tun asali ba da son ran su ba.

Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba

A wani labarin daba, mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.

Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.

Kara karanta wannan

Adamawa: ‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargin sun halaka mutum 7 da tsafi

Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel