Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto
- Fasto ya bayyana hasashensa, ya ce Najeriya za ta samu sauki nan kusa da yardar Ubangiji
- A cewarsa, daga ranar 1 ga watan Oktoba kasar za ta samu 'yancin kai na gaskiya a duniya
- Ya bayyana haka ne yayin shirin fara wani taron gumurzu da za a fara yau Juma'a a Abuja
Abuja - Babban Limami na Deeper Christian Life Ministry (DCLM), Fasto William Kumuyi, ya ce rashin tsaro, zalunci da azabtarwa duk za su kau yayin da Najeriya ke murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai na wannan shekara a ranar 1 ga Oktoba.
Kumuyi ya fadi haka ne a lokacin da ya isa Abuja don yin taron gumurzu na kwanaki 5 mai taken, “Divine Solution Global”, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma yi kira da a tattauna ko a yi zaman fahimtar juna tsakanin bangarori domin samun mafita ta dindindin a danbarwar da ke likitoci mazauna Najeriya da Gwamnatin Tarayya.
A bangare guda, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta kula da yin afuwa ga tubabbun 'yan Boko Haram da kyau domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, duba da abubuwan da suka faru a baya, ya kamata gwamnati ta sa hankali wajen tabbatar da masu tuban gaskiya da na karya cikin tubabbun 'yan Boko Haram.
Ya bayyana cewa taron gumurzun da za a fara a ranar Juma'a 24 ga Satumba, za a yi shi ne don kawo mafita ga dukkan mutane daga kuskuren da suka yi a baya saboda za a sami sauyi mai kyau ga duk wanda ya halarci taron.
A kamalan Kumuyi:
"Bayan taron, za mu sami 'yancin kanmu, na yi imanin cewa tare da mai da hankali kan mafita ta Ubangiji ga kowa da kowa, ba kawai ga mutanen da ke nan ba, za mu hadu da mutane a yanar gizo a duk fadin wannan kasar da ma duniya baki daya.
"Na yi imanin cewa yayin da muke tafiya zuwa mataki na gaba a matsayin kasa da kuma daidaikun mutane da dangi a tare, na yi imanin cewa 'yancin kai na gaske daga duk abubuwan da ke zalunta, kai hari da azabtar da rayuwar mu, za mu sami 'yanci na gaske da mafita ga kowace matsala."
Rikici ya barke tsakanin gwamnoni biyu na APC saboda dokar hana kiwo a fili
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya caccaki takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, kan kalaman da ya yi game da dokar hana kiwo a fili.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Gwamna El-Rufai ya bayyana dokar hana kiwo a fili da wasu daga cikin gwamnonin kudu ke sanyawa a matsayin abin da ba zai yiwu ba.
Sai dai Gwamna Akeredolu a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Donald Ojogo ya fitar, ya ce bai kamata irin wannan magana ta fito daga shugaba ba, inji jaridar.
Gwamna Akeredolu wanda yake jam’iyya daya da El-Rufai; jam’iyyar APC, ya zargi gwamnan na Kaduna da yin iya bakin kokarinsa wajen kai ‘yan ta’adda zuwa yankin kudanci a karkashin wani ra’ayinsa da ke kare aikata barna.
Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari
A wani labarin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi gargadin a kula game da komawar 'yan bindigan da yunwa ta fatattaka, zuwa garuruwa da yankuna don satar kayayyakin gona kafin lokacin girbi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Gwamnan ya yi gargadin ne a ranar Talata 21 ga watan Satumba, a Katsina, a wani taron shawari da ya yi da Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed kan yanayin tsaro a jihar.
Taron ya samu halartar Shugabannin hukumomin tsaro na jihar, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Asali: Legit.ng