Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa

Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa

  • Manjo Janar Christopher Musa, ya ce rundunar sojin Najeriya ba za ta bar ISWAP ta samu wurin zama a Najeriya ba
  • Ya bayyana cewa, wasu masu son ganin bayan Najeriya ne ke daukar nauyin kungiyar duk da ba ta kasar nan bace
  • Musa ya ce kungiyar basu wa Najeriya fatan alheri don haka ba za a sassauta musu ba ko kadan

Borno - Kwamandan rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai, Maj.-Gen. Christopher Musa, ya ce dakarun sojin Najeriya ba za su bar kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta samu wuri tare da yin kane-kane a Najeriya ba.

Musa ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa
Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda ya ce, ISWAP kungiyar ta'addanci ce ta ketare wacce wasu daga kasashen ketaren ke daukar nauyin ta, ta yuwu kuma akwai wasu 'yan Najeriya da ke daukar nauyin ta. Don haka ba ta da wurin zama a kasar nan.

Kara karanta wannan

Rundunar soji: Muna mutunta su ne kawai, ba tarairayar tubabbun 'yan ta'adda mu ke ba

"A bayyane ya ke cewa 'yan ta'addan ISWAP ba 'yan kasar nan bane, kawai suna shigowa ne domin tada zaune tsaye. Ba za mu kuwa lamunci hakan ba.
“A saboda hakan na ke son kara mana karfin guiwa, ballantana 'yan kasar nan da suka hada kai da su, ku sani cewa babu matsuguninsu a kasar nan.
"Ba su yi wa kasar nan fatan alheri kuma ba su yi wa kansu kuma ba za mu taba barin wani bakon haure ya shigo mana kasa ba," yace.

Kwamandan rundunar ya sanar da cewa, rundunar sojin ta shawarci gwamnati kan bukatar a fara da jama'a kan yadda za a yi da tubabbun 'yan ta'adda, Daily Trust ta wallafa.

Fusatattun 'yan fansho sun garkame SSG na Ogun kan rike N68bn na garatutinsu

Kara karanta wannan

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

A wani labari na daban, fusatattun 'yan fansho na jihar Ogun a ranar Laraba sun rufe sakateriyar jihar inda ofishin gwamnan ya ke da zanga-zanga saboda kin biyansu kudinsu har N68 biliyan kusan shekaru goma kenan da suke bin gwamnatin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan fanshon da ke karkashin kungiyar karamar hukuma sun mamaye manyan kofofi 2 na sakateriyar da ke Oke-Mosan a Abeokuta inda suka hana SSG Tokunbo Talabi da sauran ma'aikatan shiga tsawon sa'o'i hudu.

Masu zanga-zangar sun tafi dauke da takardu wadadna aka yi rubuce-rubuce daban-daban domin nuna fushinsu kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel