Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu

Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana shirin gwamnatinsa na kawo karshen ta'addanci a jihar
  • Matawalle ya bayyana hakan ne a Gusau, babban birnin Zamfara a ranar Asabar, 11 ga watan Satumba, yayin da yake jawabi ga wani taro
  • A cewarsa, hare-haren da jami'an tsaro ke kaiwa 'yan fashi ya sa sun yi kokarin neman tattaunawa da gwamnati

Gusau, Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa ba ta da sha'awar tattaunawa da 'yan bindiga, lura da cewa sun yi watsi da damar da aka taba basu.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ya bayyana a Gusau cewa maimakon haka, jami’an tsaro zasu fatattake su daga jihar.

Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu
Bello Matawalle ya ce ba zai sake yin sulhu da 'yan bindiga a Hoto: Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Matawalle ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu hakuri tare da tallafawa sabbin matakan tsaro da aka sanya domin fatattakar 'yan bindiga da abokan aikin su don dawo da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi

Yace:

"Gwamnatina ba za ta sake yin afuwa ga 'yan bindiga ba saboda sun kasa rungumar shirin zaman lafiya da aka yi musu tun farko."

Jaridar The News ta kuma ruwaito gwamnan ya ce yawan hare-haren da rundunar tsaro ke kaiwa yan bindiga ya sa sun fara kokarin neman sulhu da gwamnati.

Ya ce wakilan ‘yan fashin sun sanar da shi cewa sun tuba kuma suna son tattaunawa da gwamnati.

Matawalle ya lura cewa wasu daga cikin 'yan fashin suna ficewa daga Zamfara zuwa wasu jihohi sakamakon sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar ta bullo da su.

Amma, ya gargadi 'yan siyasa kan ba da kowane irin tallafi ga yan fashi, yana mai jaddada cewa 'yan siyasa su ji tsoron Allah su daina sayan babura don rabawa mutane da su kuma, suke sayar wa yan fashi don ci gaba da ayyukansu na mugunta.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin Zamfara za ta hukunta duk wani dan siyasa da aka kama da hannu a lamarin.

Jihar ta katse hanyar samar da abinci, da albarkatun man fetur da sauran muhimman kayayyaki ga 'yan bindigar a sansanin su.

Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa

A wani labarin, mun ji cewa rufe kasuwanni masu yawa a fadin jihohin arewa maso yamma na Najeriya ya kasance babban kalubale ga 'yan fashin daji.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a kalla gwamnonin yankin hudu ne suka umarci rufe kasuwannin jihohinsu a matsayin hanyar dakile ta'addanci.

Kwanaki kadan bayan rufe kasuwannin a wasu kayukan Sokoto, 'yan fashin daji sun fara bukatar kayan abinci a matsayin fansar wadanda ke hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel