SERAP Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Kan Datse Hanyoyin Sadarwa a Zamfara da Katsina

SERAP Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Kan Datse Hanyoyin Sadarwa a Zamfara da Katsina

  • Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban ƙasa Buhari ya gaggauta dakatar da matakin datse sabis a Zamfara da Katsina
  • A cewar kungiyar wannan matakin ya kara wa al'ummar yankin matsin rayuwa banda wanda suke ciki a baya
  • Hukumar NCC ta umarci kamfanonin sadarwa su datse hanyoyin sadarwa a Zamfara da wasu kananan hukumomi a Katsina

Abuja - Ƙungiyar dake fafutukar ganin anyi adalci a sha'anin mulki, SERAP, ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin tarayya na datse sabis ɗin sadarwa a Zamfara da Katsina, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wannan dai ya biyo bayan halin tasku da al'umma suka shiga a jihar Zamfara da wasu sassa na Katsina kan datshe hanyoyin sadarwa da FG ta yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

SERAP ta yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci ma'ikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) su yi saurin dawo da sabis a dukkan yankunan da lamarin ya shafa.

SERAP Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari
SERAP Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Kan Datse Hanyoyin Sadarwa a Zamfara da Katsina Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kungiyar ra roki shugaba Buhari kan ya gaggauta umartar ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya maida harkokin sadarwa kamar da a Zamfara da Kananan hukumomin 13 da abun ya shafa a Katsina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa aka katse sadarwa?

A kwanakin baya hukumar NCC ta umarci kamfanonin sadarwa da su dakatar da ayyukansu a faɗin jihar Zamfara, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Legit.ng hausa ta rahoto muku cewa hukumomi sun sake umartar kamfanonin su ɗauke sabis ɗin sadarwa a kananan hukumomi 13 daga cikin 34 na jihar Katsina.

Sakon SERAP ga Shugaba Buhari

Sai dai wannan matakin baiwa kungiyar SERAP daɗi ba, inda ta aike da wata wasika ga shugaba Buhari, mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Kolawole Oluwadare.

Kara karanta wannan

Hukumar ICPC ta kwato garkame kadarori da dan majalisar Yobe ya boye na mazabarsa

Wani sashin wasikar yace:

"Datse sabis da sauran harkokin sadarwa a Jihohin Zamfara da Katsina, ba tare da wata kwakkwarar hujja ba ya saba wa doka da hankalin duk wani mai tunani."
"Katse hanyoyin na sadarwa wani mataki ne na hukunta ’yan Najeriya da ke zaune a waɗannan yankuna duk kuwa da yanayin matsi da suke ciki tun asali."

A wani labarin kuma Mutane da dama sun mutu yayin da yan bindiga daga Zamfara da Katsina suka faɗa sansanin Sojoji

Cikin rashin sani wasu miyagun yan bindiga da suka tsero daga Zamfara da Katsina sun faɗa cikin sansanin sojoji.

Rahoto ya bayyana cewa an ɗauki dogon lokaci ana fafatawa tsakanin miyagun da sojoji a ƙauyen Maganda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262