Ruwan Bama-Bamai Ba Kakkautawa: Kashi Na Biyu Na Jiragen Yaƙin A-29 Super Tucano Sun Nufo Najeriya

Ruwan Bama-Bamai Ba Kakkautawa: Kashi Na Biyu Na Jiragen Yaƙin A-29 Super Tucano Sun Nufo Najeriya

  • Rahotanni sun bayyana cewa jiragen yaƙi guda 6 ƙirar A-29 Super Tucano da Najeriya ta siya daga Amurka sun taho Najeriya
  • Tun a watan Fabrairun 2018 ne gwamnatin Najeriya da siya jiragen guda 12 kan kudi dala miliyan $496m
  • A watan Yuli, 2021, jirage 6 daga cikin 12 a rukunin farko suka iso ga rundunar sojojin saman Najeriya

Abuja - Kashi na biyu na jiragen yaƙi guda 6 ƙirar 'A-29 Super Tucano' sun baro ƙasar Amurka, sun kamo hanyar zuwa Najeriya.

Mai taimakawa shugaban ƙasa ta ɓangaren yaɗa labarai, Tolu Ogunlesi, shine ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

A wani rubuta da ya tura a shafinsa daga Telegram, Ogunlesi ya bayyana cewa jiragen yaƙin sun tsaya a Rectrix domin zuba musu mai zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Wajibi Yan Najeriya Su Taimaki FG Wajen Yaki da Matsalar Tsaro a Najeriya, Sanata Lawan

Jirgin yaƙin Super Tucano
Ruwan Bama-Bamai Ba Kakkautawa: Kashi Na Biyu Na Jiragen Yaƙin A-29 Super Tucano Sun Nufo Najeriya Hoto: Tolu Ogunlesi FB Fage
Asali: Facebook

Yaushe zasu iso Najeriya?

Rahotanni sun nuna cewa ana tsammanin jiragen zasu dira a ƙasa Najeriya a tsakanin 24 ga watan Satumba da muke ciki.

Yace:

"Jiragen sun sauka a filin sauka da tashin jirage na Worcester Regional dake Rectrix domin duba lafiyarsu da kuma ƙara mai."
"Rundunar sojojin sama sun jima suna amfani da jiragen yaƙi na A-29 Super Tucano wajen yaƙi da yan ta'adda."

Ambasadan Amurka a Najeriya ta ziyarci matuƙa jirgin

Rahoto ya bayyana cewa ambasadan ƙasar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ta je mahaifarta Worcester domin halartar wani taro a makarantar Doherty Memorial High School.

Leonard ta ziyarci matuƙa jiragen yaƙin, waɗanda zasu taho da jiragen zuwa Najeriya domin ganin tashin su, ranar Alhamis.

Yaushe Najeriya ta siyo jiragen?

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sayi jiragen yaƙi 12 na Super Tucano a kan kuɗi dala miliyan $496m tun a watan Fabrairun 2018.

Kara karanta wannan

Hotunan shugaba Buhari yayin da yake hawa jirgi zuwa kasar Amurka

Bugu da ƙari, kashi na farko na jiragen guda 6 sun iso ga rundunar sojin sama a ranar Alhamis 22 ga watan Yuli.

FG ta fara biyan ma'aikatan N-Power

A wani labarin kuma Labari Mai Dadi, Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara biyan ma'aikatan N-Power haƙƙoƙinsu da ta rike a baya.

Sakataren dindindin na ma'aikatar jin ƙai da walwala, Bashir Alkali, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar

Yace ma'aikatan sun fara ganin saƙon shigar kuɗi a asusun bankin su na watanni biyar (N150,000).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262