Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba

Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba

  • Jami'an lafiya tare da haɗin kan jami'an tsaro sun fara aiwatar da umarnin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki kan rigakafin korona
  • Gwamnan ya sanar da shirin gwamnatinsa na dakatar da duk wani ma'aikaci da bai yi allurar rigakafin COVID19 ba daga zuwa aiki
  • Wasu hotuna da suka fito daga jihar sun bayyana yadda ma'aikata ke nuna katin shaida kafin shiga kowace ma'aikata a Benin

Edo - Gwamnatin jihar Edo, karkashin jagorancin gwamna Obaseki ta fara aiwatar da dokar "Ba rigafin korona, babu aiki" a ma'aikatun jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna Obaseki na jihar Edo, shine gwamna na farko a Najeriya da ya hana mutanen da ba'a musu rigakafin cutar COVID19 ba shiga wuraren gwamnati.

Duk da cewa da farko an yi watsi da kudirin gwamnan, amma Obaseki bai yi kasa a guiwa ba wajen aiwatar da kudirinsa.

Hotuna daga Edo
Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Su wa ke hana mutane shiga ma'aikatu?

A ranar Laraba da safe, jami'an lafiya da kuma jami'an tsaro sun kafa madakata a kofar shiga ma'aikatun Benin, Babban birnin jihar, inda suke tabbatar da an bi umarnin gwamna.

Hotunan yadda lamarin ke faruwa

Hotuna daga Edo
Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hotuna daga Edo
Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hotuna daga Edo
Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hotuna daga Edo
Hotunan Yadda Gwamna Ya Hana Ma'aikata Shiga Wurin Aiki Matukar Basu Yi Allurar Rigakafin COVID19 Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ba damar shiga sakateriyar gwamnati a Edo sai da kati

Punch ta ruwaito cewa an hana duk wani ma'aikaci da ya gaza gabatar da katin shaidar allurar rigakafin COVID19 shiga sakateriyar gwamnatin Edo.

Gwamnatin ta fara aiwatar da shirinta na hana taruwar mutane da yawa ba tare da shaidar karɓar rigakafi ba.

Lamarin wanda ya fara da karfe 7:00 na safiyar Laraba, yasa an hangi shugaban kwamitin yaƙi da COVID19 na jihar, Yusuf Haruna, ya tare babbar kofar shiga sakateriyar wacce ta yi hannun riga da ofishin EFCC.

A wani labarin kuma Wani Mai Motar Alfarma Ya Shararawa Ɗan Keke Nafef Mari Kan N500, Mutumin Ya Mutu

Wani mai motar alfarma da bata jin harsashi ya shararawa direban keke Nafef mari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa a Ilorin.

Rahotanni sun nuna cewa ɗan nafef ɗin ya yi wa mai motar laifi na fasa masa fitila ta kimanin N2,500, amma ya nemi alfarmar zai biya N2,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel