Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

  • Miyagun 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe shugaban cocin Anglika, Emeka Merenu a Imo
  • Kamar yadda aka gano, an zargi 'yan ta'addan ESN da bindige shi har lahira saboda ya kira sojoji tsaron cocinsa da makaranta
  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Nkwerre ta jihar Imo ya tabbatar da aukuwar mummunan lamarin

Imo - A ranar Talata 'yan bindiga sun harbe wani shugaban cocin Anglika mai suna Emeka Merenu, dan asalin kauyen Amorji Agbomiri da ke karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo.

Daily Trust ta wallafa cewa, an zargi cewa wasu 'yan kungiyar ESN da ke da alaka da masu rajin kafa kasar Biafra da harbe shi.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo
Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo
Asali: UGC

Dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Nkwerre da ke jihar Imo, Obinna Okwara, ya tabbatar wa da manema labarai aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Kamar yadda ya ce, Rabaren Emeka Merenu an kashe shi a gidan cocin da ke Orsu Iheteukwa da ke karamar hukumar Orsu ta jihar Imo a sa'o'in farko na ranar Talata.

Ya ce an sheke limamin ne kan zarginsa da ake da kawo sojoji domin gadin cocinsa da kuma makarantar sakandare da ke karkashin kulawarsa.

Dan majalisar ya kara da cewa, miyagun ba su bar hatta motarsa ba, sai da suka banka mata wuta, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Har a halin yanzu ba a samu kakakin rundunar 'yan sandan jihar, CSP Mike Abattam domin tsokaci.

Damfarar daukar aiki: An dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjayen majalisar Nasarawa

A wani labari na daban, majalisar jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba wanda aka fi sani da PDP-Obi 2 kan zarginsa da ake da daukar aikin bogi na malamai 38 na makarantun sakandare a jihar.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya sanar da wannan yayin zaman majalisar a ranar Litinin a Lafia.

Dakatar da Zhekaba ya zo ne bayan majalisar ta tattauna kan rahoton kwamitin ilimi na majalisar kan daukar aikin malamai 366 da wasu 38 na bogi da aka gani wurin jerin biyan kudin albashi na jihar.

Kakakin majalisar ya kafa kwamitin mutum uku na wucin-gadi domin bincikar dakataccen dan majalisar kuma a kawo rahoto gaban majalisar nan da makonni biyu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel