Yanzu-Yanzu: Gwamna ya haramtawa ma'aikata zuwa aiki har sai sunyi riga-kafin korona

Yanzu-Yanzu: Gwamna ya haramtawa ma'aikata zuwa aiki har sai sunyi riga-kafin korona

  • Gwamnatin jihar Edo ta saka dokar hana ma'aikata zuwa ofis idan ba su yi riga-kafin korona ba
  • Gwamnatin ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Satumban 2021 a dukkan fadin jihar
  • Saka dokar ya biyo bayan yawan mutane da ke kamuwa da cutar ta korona da mutane ne a jihar ta Edo

Jihar Edo - Gwamnatin Jihar Edo ta haramtawa ma'aikatan da ba su yi allurar riga-kafin korona ba shiga ofishosinsu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin ta hana dukkan wadanda ba su riga sun yi riga-kafin ba shiga wuraren taruwan mutane.

Yanzu-Yanzu: Gwamna ya haramtawa ma'aikata zuwa aiki har sai sunyi riga-kafin korona
Gwamna ya haramtawa ma'aikata zuwa aiki har sai sunyi riga-kafin korona. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Tunda farko, Gwamna Godwin Obaseki, a cikin watan Satumba, ya hana wadanda ba a yi wa rigakafi shiga bankuna, ofisoshin gwamnati da wuraren ibada.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun banka wuta gidan Kakakin majalisar wakilan jihar Zamfara

Hakan ya janyo cece-kuce inda wata kungiya ta tafi domin hana aiwatar da dokar amma gwamnan bai sauya ra'ayinsa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yaushe dokar za ta fara aiki?

A ranar Talata, sakataren dindindin na ma'aikatar lafiya na jihar Edo, Osamwonyi Irowa, ya ce daga ranar 15 watan Satumban 2021 ya ce gwamnatin za ta aiwatar da dokar 'babu katin riga-kafi, ba shiga wuraren taruwan jama'a'.

Ya ce:

"Idan za ku shiga sakatariyar jiha ko wasu ofisoshin gwamnati, ya zama dole ku kasance kuna dauke da katinku na yin riga kafin annobar korona.
"Za a fara aiwatar da dokar gobe 15 ga watan Satumba za a fara ne da hukumomin gwamnati.
"Wadanda ba su iya nuna katinsu na riga-kafin COVID-19 ba za su yi mana uzuri su rika aiki daga gidajensu har zuwa lokacin da za a cimma matsaya A matsayin mu na jiha, muna yin duk abin da ya dace don ganin cutar bata yadu ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

"Muna kira ga mutanen mu su yi riga-kafin saboda ya fi dacewa wurin kiyayye cutar da mutuwa. Tawagar masu dubawa za su fara aiki gobe don taimaka mana rage adadin sabbin masu kamuwa da wadanda ke mutuwa a kullum."

An nada tawaga 20 da za su saka ido kan ganin an bi dokar

Yusuf Haruna, shugaban tawagar masu tabbatar da an yi riga kafin ya ce an bawa tawaga 20 horaswa domin su tabbatar sai wanda ya yi riga kafin zai shiga ofisoshin gwamnati.

Kawoo yanzu, an samu mutane 1,034 masu dauke da cutar a jihar Edo sannan ta kashe mutane 53 a zango na uku na annobar ta COVID-19.

A cewar gwamnatin jihar, mutane 20 da ba su yi rigakafin ba sun mutu a kwanaki hudu da suka gabata.

Bidiyon katon din giya 3,600 da Hisbah ta kama an ɓoye cikin buhunan abincin kaji a Kano

A wani rahoton daban, hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani babban mota makare da kiret din giya daban-daban da aka boye su cikin buhunnan abincin kaji, SaharaReporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

A cikin wani faifan bidiyo da LIB ta wallafa, an gano babban kwamandan Hisbah, Harun Ibn Sina da wasu ma'aikatan hukumar suna bude zakulo kwalaben giyan da aka boye a motar da ke dauke da abincin kaji.

An ruwaito cewa motar ta taso ne daga Kwanar Dangora tana kan hanyar ta na zuwa garin Kiru a Jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164