Gwamna Ya Bi Sahun Tinubu, Ya Fara Rabawa Mutane Tallafin N50,000

Gwamna Ya Bi Sahun Tinubu, Ya Fara Rabawa Mutane Tallafin N50,000

  • Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu ya fara rabon tallafin N50,000 ga mutane 29,400 masu ƙaramin ƙarfi a faɗin jihar
  • Bayanai sun nuna cewa za a daukimutum 150 daga kowace mazaba cikin mazabu 196 na jihar, wadanda za a bai wa wannan tallafi
  • Masu cin gajiyar shirin sun haɗa da mutane 100 a ƙarƙashin shirin tallafin kuɗi da kuma ƙwararru 50 da ke buƙatar jari don kafa ko faɗaɗa sana’o’insu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Gwamnatin Jihar Cross River karkashin jagoranci Gwamna Bassey Otu ta fara raba tallafin N50,000 ga kowane mutum daga cikin mutane 29,400 da aka zaɓo.

Bayanai sun nuna cewa gwammatin ta zabo mutane 29,400 masu ƙaramin ƙarfi, ƙarƙashin Shirin Zuba Jari a Fannin Jin Ƙai (SIP) na jihar Cross River.

Kara karanta wannan

Mutanen Kano na cikin alheri, Gwamna Abba ya shirya rabon tallafin N50,000

Gwamna Otu.
Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu a gidan gwamnatinsa da ke Calabar Hoto: Governor Bassey Otu
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta rahoto cewa mai kula da shirin a jihar, Dakta Edem Okokon Effiom, ne ya bayyana hakan a Calabar ranar Talata da ta gabata.

Ya ce an fara biyan kuɗin ne kimanin kwanaki biyar da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar da aikin domin tabbatar da kowane mutum da za a zaba ya samu tallafin N50,000.

Effiom ya ce shirin zai shafi dukkan mazabu 196 na jihar, inda za a zaɓi mutane 150 daga kowace mazaba domin amfana da tallafin.

Ya bayyana cewa waɗanda za su amfana sun haɗa da mutane 100 da ke ƙarƙashin ɓangaren shirin tallafi na CCT, da kuma masu kwarewa 50 da ke buƙatar tallafin kuɗi domin kafa ko faɗaɗa sana’o’insu.

Yadda ka zabi wadanda aka ba kudin

Mai kula da shirin ya bayyana cewa an fara gina kundin sunayen waɗanda za su amfana tun daga watan Yuni na 2026, inda aka yi ƙoƙarin tabbatar da cewa an shigar da mutane daga sassa daban-daban.

Kara karanta wannan

Barayi sun shiga masallaci sun sace fankoki sama da 20 a Kano

Ya ce tsarin zaɓen ya ƙunshi gano masu ƙaramin ƙarfi ta hannun cibiyoyin addini da na gargajiya, ƙungiyoyin mata, ƙungiyoyin matasa da sauran rukunin jama’a da za a iya tantancewa.

Effiom ya fayyace cewa kuɗin N50,000 da wasu mazauna jihar ke karɓa, tallafi ne da gwamnatin Cross River ta bayar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bassey Otu.

Ya yi wannan bayani ne bayan samun ruɗani sakamakon yaɗuwar wani shirin tallafin kuɗi makamancin haka a kafafen sada zumunta.

Cross River.
Taswirar jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An fara samun korafe-korafe

Dangane da korafe-korafen mutanen da ba su karɓi kuɗinsu ba tukuna, Effiom ya danganta wasu daga cikin jinkirin da matsalolin da suka shafi bayanan asusun banki da Lambobin BVN.

Ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa jami’an da abin ya shafa na aiki don magance matsalolin, domin tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci tallafin ya karɓi haƙƙinsa.

Gwamna Otu ya tir da harin Peter Obi

Kun ji cewa gwamnan jihar Cross River, Sanata Bassey Otu, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso a Calabar.

Gwamna Otu ya umarci jami’an tsaro su gano waɗanda suka aikata harin kuma su kama su domin su girbi abin da suka shuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262