"Karya Suke Yi": Tinubu Ya Sake Magana kan Dawo da Tallafin Fetur
- Tinubu ya bayyana cewa babu shirin dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa gwamnati za ta mayar da hankali kan ilimi da noma
- Ya yi alƙawarin ba manoma ƙananan gonaki rancen kuɗi ba tare da ruwa ba, tare da kafa cibiyoyin aikin noma na zamani a wurare shida
- Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ta ƙarfafa rundunar ’yan sanda da sojoji, tare da ƙara musu albashi domin yaƙi da rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Jigawa - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tallafa wa manoma da bunƙasa ilimi.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Dutse Township Stadium da ke Jihar Jigawa, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Gangamin na daga cikin jerin tarukan yaƙin neman zaɓen da APC ke gudanarwa a faɗin ƙasar gabanin babban zaɓen 2027.
Tinubu ya ce ba za a dawo da tallafin fetur ba
Yayin da yake magana kan batun tallafin man fetur, shugaban ƙasar ya musanta ikirarin cewa gwamnatinsa za ta dawo da shi.
Ya ce bai kamata a riƙa kashe kuɗaɗen da ya kamata a tanada domin makomar yara wajen biyan tallafin man fetur ba, maimakon mayar da su kan ilimi da noma, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
"Ga waɗanda ke cewa za a dawo da tallafin man fetur, ƙarya suke yi. Kada ku sake yarda a yaudare ku. Ba za a dawo da shi ba.
“Ba za mu iya kashe makomar ’ya’yanmu a yau, sannan mu yi tsammanin za su samu ci gaba a gobe ba. Dole ne su kasance a makaranta. Dole ne mu zuba jari a iliminsu da kuma harkar noma.” In ji shi.

Kara karanta wannan
Shugaban APC ya fito da magana kan batun Tinubu bai da lafiyar tsayawa takara a 2027
Kananan manoma za su samu tallafi
Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da tallafi ga manoma, musamman waɗanda ke noma a ƙananan gonaki.
Ya ce gwamnati za ta ba su rancen kuɗi ba tare da amsar kudin ruwa ba, domin taimaka musu su faɗaɗa ayyukan noma da samar da abinci.
Shugaban ƙasar ya kuma bayyana shirin kafa cibiyoyin samar da injinan noma na zamani a wurare shida na ƙasar domin sauƙaƙa wa manoma gudanar da ayyukansu.
“Za mu tallafa wa noma, za mu kuma ba manoma ƙananan gonaki lada. Ana shirin samar da rance ba tare da ruwa ba ga manoma. Wadata za ta zo, kuma za a samu wadatar abinci.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa za a kafa cibiyoyin hidimar aikin noma da injina a wurare shida na ƙasar.
Tinubu ya yi alƙawari kan noma
Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa jami’o’in Najeriya za su taka rawa sosai wajen bincike da bunƙasa sabbin hanyoyin noma.

Kara karanta wannan
Tsohon abokin takarar Buhari ya bayyana dalilin kin karbar tayin mukamin da Tinubu ya yi masa
Ya ce gwamnatinsa za ta ƙarfafa haɗin gwiwar jami’o’i da ɓangaren noma domin samar da hanyoyin da za su inganta yawan amfanin gona.

Source: Facebook
Atiku ya soki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubaka ya jaddada rashin amincewarsa da shirin gwamnatin tarayya na neman sabon bashi na dalar Amurka miliyan 500 daga Bankin Duniya.
Atiku ya bayyana cewa bai kamata shugaba Bola Tinubu ya kulla alƙawarin sabon bashi ba a daidai lokacin da yake shirin mika mulki a shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
