Wani Mai Motar Alfarma Ya Shararawa Ɗan Keke Nafef Mari Kan N500, Mutumin Ya Mutu
- Wani mai motar alfarma da bata jin harsashi ya shararawa direban keke Nafef mari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa a Ilorin
- Rahotanni sun nuna cewa ɗan nafef ɗin ya yi wa mai motar laifi na fasa masa fitila ta kimanin N2,500, amma ya nemi alfarmar zai biya N2,000
- Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin a yankin Garin Alimi, Ilorin
Kwara - Wani direban motar alfarma wadda harsashi baya ratsa ta, Kayode Oluwatomi, ya laƙaɗawa ɗan nafef, Kola Adeyemi, duka har ya mutu a Ilorin jihar Kwara, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa direban Nafef ɗin ya buga wa mutumin, lamarin da ya jawo lalacewar fitilar yin fakin.
Legit.ng Hausa ta gano cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a yankin Gerin Alimi, cikin garin Ilorin.
Mai Nafef, Adeyemi, ya bugi motar ta alfarma mai lamba BX 954 AJL a baya, lamarin da ya jawo fasa fitilar aje mota, wanda ake siyarwa N2,500.
Shin ɗan nafef din ya biya kuɗin?
Wani shaidan gani da ido, wanda ya ɓoye sunansa, yace direban nafef ya roki alfarma zai biya N2,000 na ɓarnar da yayi, amma mai motar yaƙi amincewa.
Mutumin yace:
"Nan take rikici ya ɓarke tsakaninsu, mai motar ya ɗaga hannu ya mari ɗan nafef ɗin da wani abu da ake zargin zobe ne ko laya, nan take ya faɗi kasa warwas."
"Daga baya an tabbatar da ɗan nafef ɗin ya rigamu gidan gaskiya a asibitin Garin Alimi dake Ilorin."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Yace mataimakin shugaban ƙungiyar direbobin keke nafef, Ganiyu Adebayo, ya kawo wa yan sanda rahoton yadda lamarin ya faru tsakanin mai motar da kuma ɗan nafef.
A wani labarin kuma Ministan Buhari ya fallasa yadda ake amfani da jiragen alafarma wajen satar albarkatun Zinari a Najeriya
Ministan hakar albarkatun ƙasa, Dakta Uche Ogah, ya bayyana irin ta'adin da ake yi ta hanyar amfani da jirage masu zaman kansu.
Ogah yace dole sai an samar da hukunci mai tsauri kan duk waɗanda aka damke da hannu a safarar zinari ba bisa ka'ida ba.
Asali: Legit.ng