An Fara Nuna Yatsa ga Shugaban APC da Jam'iyyar ke Fuskantar Rikici a Zamfara
- Hassan Umar Dangaladima ya shigar da ƙorafi ga shugabannin APC na ƙasa, yana zargin Nentawe Yilwatda da nuna son kai
- Ɗan takarar ya ce an kafa kwamitin zaɓe ba tare da amincewar NWC ba, yana zargin wasu mambobinsa da goyon bayan Aminu Sani Jaji
- Sai dai Yilwatda ya musanta zargin, yana mai cewa dukkan matakan da jam’iyyar ke ɗauka ana yanke su ne bisa shawarar shugabannin NWC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Rikicin cikin gida da ke addabar APC a Zamfara ya ƙara tsananta bayan wani ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ya shigar da ƙorafi kan shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nentawe Yilwatda.
Ɗan takarar, Hassan Umar Dangaladima, ya zargi Yilwatda da nuna son kai wajen kafa kwamitin da zai gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani na mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji.

Source: Twitter
Dangaladima ya miƙa ƙorafin ga kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), yana neman su shiga tsakani domin tabbatar da adalci a zaɓen.
Wannan na zuwa ne bayan umarnin kotu na sake gudanar da zaɓen fidda gwanin domin fitar da ɗan takarar APC a mazabar, cewar The Sun.
Zargin kafa kwamitin zaɓe
A cikin ƙorafinsa, Dangaladima ya yi iƙirarin cewa Yilwatda ya kafa kwamitin gudanar da zaɓen ba tare da kiran taron NWC ko neman amincewar sauran shugabannin jam’iyyar ba.
Ya bayyana cewa ba a tattauna batun kafa kwamitin a gaban mambobin NWC ba, haka kuma ba a gabatar da sunayen waɗanda za su gudanar da zaɓen domin samun sahalewar kwamitin ko NEC ba.
Ɗan takarar ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin mutanen da aka naɗa a kwamitin na da alaƙa ta siyasa da babban abokin hamayyarsa, Aminu Sani Jaji.
Zargin Aminu Jaji ba dan APC ba ne
Wani babban batu da Dangaladima ya gabatar a ƙorafin shi ne ikirarin cewa Aminu Sani Jaji ba cikakken ɗan APC ba ne, domin babu sunansa cikin rajistar mambobin jam’iyyar a mazabar Birnin Magaji.
Ya ce kwafin rajistar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar da sahihancinsa ya nuna cewa ba a saka sunan Jaji cikin jerin mambobin jam’iyyar na mazabar ba.
Dangaladima ya kuma bayyana cewa lauyoyinsa daga kamfanin Trinity Chambers, ƙarƙashin jagorancin D.C. Enwelum, SAN, sun aika wa APC takardar neman bayani kan lamarin tun ranar 4 ga Nuwamba, 2026.
Saboda haka, ya ce bai kamata Jaji ya shiga sabon zaɓen fitar da gwanin ba idan har ba ya cikin sahihin rajistar mambobin APC.
Yilwatda ya musanta zargin nuna son kai
A nasa martanin, shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai cewa ba su da tushe.
Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Abimbola Tooki, ya bayyana cewa zargin cewa shugaban jam’iyyar na ɗaukar matakai shi kaɗai ba tare da shawarar NWC ba, ba gaskiya ba ne.
Ya ce kwamitin NWC na gudanar da ayyukansa ne ta hanyar tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin mambobinsa, inda ake yanke shawara bisa muradun jam’iyyar.
Nentawe ya ba yan adawa shawara
Mun ba ku labarin cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bukaci 'yan adawa su daina sukar gwamnati kawai.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce ya kamata 'yan siyasa su gabatar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin Najeriya.
Yilwatda ya ce cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewar kasafin kudi.
Asali: Legit.ng


