An Kwayewa PDP, ADC Zani a Kasuwa Kwanaki Kaɗan bayan zuwa Atiku

An Kwayewa PDP, ADC Zani a Kasuwa Kwanaki Kaɗan bayan zuwa Atiku

  • Wasu mambobin kwamitin gudanarwar PDP na jiha uku da shugabannin ƙananan hukumomi bakwai sun fice daga jam’iyyar zuwa APC a Sokoto
  • Tsoffin jiga-jigan PDP da ADC sun ce sun yanke shawarar komawa APC ne saboda yadda Gwamna Ahmed Aliyu ke tafiyar da mulkinsa
  • APC ta karɓi sababbin mambobin tare da buƙatar su yi amfani da tasirinsu wajen yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Wasu manyan ‘yan siyasa a jihar Sokoto sun fice daga jam’iyyun PDP da ADC tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki a matakin jiha.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai mambobi uku na kwamitin gudanarwar PDP na jihar, shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomi bakwai, da wasu shugabannin matasa da mata.

APC ta yi babban kamu a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto. Hoto: Ahmed Aliyu.
Source: Facebook

Haka kuma, wasu fitattun ‘yan jam’iyyar ADC sun bi sahunsu wajen komawa APC a wani mataki da ya ƙara sauya fasalin siyasar jihar gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta ragargaji APC kan hukuncin rusa takarar Atiku a kotu

Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Faruku Labbo, ne ya karɓi waɗanda suka sauya sheƙar a madadin jam’iyyar APC.

Da yake magana a madadin tsoffin mambobin PDP, Shehu Abdullahi Mai Rago ya ce sun yanke shawarar komawa APC ne saboda yadda suke kallon salon shugabancin Gwamna Ahmed Aliyu.

Ya bayyana cewa gwamnan ya nuna musu mutunta ra’ayoyin siyasa, duk da cewa a baya suna cikin jam’iyyar adawa a jihar.

Mai Rago ya ce:

“Duk da cewa a baya muna cikin jam’iyyar adawa a jihar, Gwamna Ahmed Aliyu bai taɓa amfani da mulkinsa wajen gallaza mana ko tsangwamar mu ba. Wannan na daga cikin manyan dalilan da suka sa muka yanke shawarar shiga APC.”

Ya kuma bayyana gwamnan a matsayin mutum mai sauƙin kai da girmama mutane, yana mai cewa manufofinsa sun haɗa da inganta rayuwar al’ummar jihar ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke ciki ba.

Baya ga haka, ya yaba da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin ke gudanarwa a fannoni daban-daban, yana mai cewa hakan ya ƙarfafa musu gwiwar mara wa gwamnan baya.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fitar da sanarwa ga shugabannin ADC da aka rusa takarar Atiku

Sun yi alƙawarin jawo sauran shugabannin PDP

Sababbin mambobin APC ɗin sun bayyana aniyarsu ta yin amfani da goyon bayan da suke da shi a yankunansu domin ƙara wa jam’iyyar ƙarfi.

Sun kuma yi alƙawarin shiga tsakanin sauran shugabannin PDP na ƙananan hukumomi domin ganin sun bi sahunsu wajen komawa jam’iyyar APC.

A nasa jawabin, Faruku Labbo ya yi maraba da sababbin mambobin, inda ya buƙace su da su yi amfani da hanyoyin sadarwarsu da magoya bayansu wajen ƙarfafa jam’iyyar a matakin ƙasa.

Ya ce suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen shirya APC domin tunkarar zaɓukan 2027, tare da tabbatar musu cewa za a ba su dama su taka rawa a harkokin jam’iyyar. Jerin waɗanda suka fice daga PDP

Rahoton ya ambaci Aliyu Mai Shinkafa, mamba a kwamitin gudanarwar PDP na jihar daga ƙaramar hukumar Binji, da Mohammed Yusuf, shugaban PDP na Kware, a cikin waɗanda suka sauya sheƙar.

Sauran sun haɗa da Altine Gudu na Gudu, Manir Tureta na Tureta, Abubakar Ango Bodinga na Bodinga, Mu’awiyya Noma na Tangaza da Muntari Dan Dare na Silame.

Kara karanta wannan

Wike ya tada wa gwamnonin APC 3 hankali da yan takaran da ya kawo jihohinsu

Haka kuma, Bello Garba Iya, sakataren PDP a Sabon Birni, da Almustafa S. Tudu, sakataren jam’iyyar a Tambuwal, na cikin waɗanda suka bar jam’iyyar.

An kuma ambaci Ahmed A. Umar da Garba Iya a cikin jerin waɗanda suka sauya sheƙar.

A ɓangaren matasa da mata kuwa, waɗanda suka koma APC sun haɗa da Balkisu Yusuf, shugabar matasan PDP a Sokoto ta Arewa, da Naja’atu Buhari, shugabar matasan jam’iyyar ta jiha.

Sauran sun haɗa da Bilkisu Sidi, shugabar mata a unguwar Waziri B, da Sadiya Umar, shugabar matan Zawarawa.

Wasu shugabannin ADC ma sun koma APC

A wani ɓangaren kuma, wasu mambobin ƙungiyar Amalgamated Association of ADC Traders, Youths and Students Stakeholders, da shugabannin ADC na unguwar Tudun Wada, sun shiga APC.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai Alhaji Shehu Jalka na Tudun Wada B da Alhaji Badamasi na Magajin Rafi B.

'Tsofaffin mambobin ADC ɗin sun bayyana cewa ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Ahmed Aliyu ke gudanarwa ne suka ƙarfafa musu gwiwar shiga APC.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ne ya sanar da sauya shekar a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Abin da ƴan Kwankwasiyya suka ce da kotu ta rushe takarar su Atiku

Wannan sauya sheƙa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen faɗaɗa sansanoninsu da tattara magoya baya gabanin babban zaɓen 2027.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.