2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

  • Gwamna Dave Umahi ya sake yin Allah wadai da jerin tattaunawar da ake yi game da zabubbukan 2023 a kasar
  • Gwamnan jihar Ebonyi ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Umahi ya bayyana cewa ya yi wuri da za a fara irin wannan tattaunawar har ma da jan hankali sosai, inda ya bukaci takwarorinsa da su mai da hankali kan abubuwan ci gaba

Ebonyi - Yayin da yakin neman zaben shugaban kasa ke kara ta'azzara a kowace rana, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce ya yi wuri da yawa da za a fara kira ga shugabancin Igbo a 2023.

Leadership ta ruwaito cewa ya yi wannan bayanin ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili
Gwamna Dave Umahi ya ce yayi wuri da za a fara tattauna batun shugabancin Ibo na 2023 Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Umahi ya shawarci gwamnonin kudu maso gabas da gwamnonin APC da su mayar da hankali kan ayyukan da za su kawo ci gaba a jiharsu, yankinsu da ma kasa baki daya.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“To, a gare ni, Na fi zurfafa ga kammala ayyukana. Kuma zan duba harkokin siyasa lokacin da wa’adin mulki na ya cika shekara daya, wanda zai kasance daga ranar 29 ga Mayu, 2022. Kuma ina tsammanin hakan yake ga sauran gwamnonin Kudu maso Gabas da gwamnonin APC.”

Idan za a iya tunawa Gwamna David Umahi ya ce ana bukatar zabin Allah don Igbo su samar da shugaban Najeriya a 2023, Premiumtimes ta kuma ruwaito.

Ya kara da cewa an kara samun kiraye-kiraye kan wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari ya fito daga Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Allah zai bamu shugaba kamar Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

A wani labarin, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana fatan wanda ke da “kyakkyawar zuciya” kamar Shugaba Muhammadu Buhari zai fito a matsayin wanda zai maye gurbinsa a 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Ya fadi hakan ne duk da cewar ya ce ya yi wuri sosai da za a shiga harkokin siyasar 2023 kamar yadda ya lura cewa hakan zai zama shagala a bangaren shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel