Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Duk da cewa wa'adin mulkinsa ya fara gangarawa, amma a kwanan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya kori wasu daga cikin wadanda ya nada tare da nada sabbin jini a matsayin wadanda za su maye gurbinsu.

Da yake bayyana dalilin da ya sa shugaban ya dauki wannan matakin, mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya ce shuganan ya ji akwai bukatar hada karfi kan “jajircewar aiki” a cikin majalisar ministocinsa don haifar da da mai ido a karshen zangon mulkinsa.

Bincike: Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora a 2021
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta ruwaito a baya, ga jerin jiga-jigai a gwamnatin nasa da ya yi waje dasu kamar haka:

1. Saleh Mamman

Har zuwa lokacin da aka sallame shi, Saleh Mamman ya kasance ministan wutar lantarki. An nada shi ya shugabanci ma'aikatar jim kadan bayan sake zaben Shugaba Buhari a wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan

Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sanar da sallamar tasa a ranar Laraba, 1 ga watan Satumban wannan shekarar.

2. Sabo Nanono

Sabo Nanono ya kasance ministan noma da raya karkara har zuwa lokacin da aka sallame shi wanda aka sanar da korarsa a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba 2021.

Sai dai fadar shugaban kasa ta ce ba a kori Mamman da Nanono ba saboda rashin aiki tukuru kamar yadda ake zargi a wasu bangarori.

3. Basheer Mohammed

A ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, shugaba Buhari ya kori Basheer Mohammed a matsayin babban darakta na hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP).

Shugaban ya hanzarta nada Fatima Waziri-Azi a matsayin sabuwar babbar darakta. Ba a bayyana dalilin daukar matakin na shugaba Buhari ba.

4. Armstrong Idachaba

A watan Yuni, Shugaba Buhari ya kori Armstrong Idachaba a matsayin babban darakta na hukumar yada labarai ta kasa (NBC), Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotunan lokacin da ministan noma ke zaune a ofis dab da isowar sanarwar korarsa

Tuni aka maye gurbinsa da Balarabe Ilelah, tsohon ma'aikacin yada labarai.

5. Farfesa Sani Mashi

A watan Maris, Shugaba Buhari ya cire Farfesa Sani Mashi daga mukamin darakta janar na Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET).

A cewar PM News, Mashi wanda ya kamata wa'adinsa ya kare a watan Janairun 2022 an maye gurbinsa da Farfesa Bako Mansur Matazu.

Korar minostocin Buhari: APC ta ce a maye gurbin Sale Mamman da dan jihar Taraba

A wani labarin daban, Jam'iyyar APC mai ci a jihar Taraba ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bai wa jihar mukamin minista a madadin tsohon ministan wutar lantarki Sale Maman wanda aka cire kwanan baya.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Ibrahim El-Sudi ne ya yi wannan kiran lokacin da yake zantawa da Daily Trust a Jalingo ranar Lahadi 5 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Rigingimu 10 da suka jawo Sabo Nanono da Saleh Mamman suka rasa kujerun Ministoci

Ya ce Taraba ta cancanci mukamin minista saboda jihar jiha ce da APC ke mulka.

El-Sudi ya bayyana cewa APC a jihar ta bai wa shugaba Buhari kuri'u sama da kashi 45 cikin dari a lokacin zaben shugaban kasa da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.