Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Kan Mu Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023

Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Kan Mu Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023

  • Gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko karkashin PDP sun bayyana shirin da suke na kwace mulki daga hannun APC
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal, yace yanzun kansu a haɗe yake kuma zasu ceto Najeriya daga APC
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnonin sun shafe awanni 7 suna tattaunawa kan rikicin dake faruwa a cikin PDP

Abuja - Gwamnonin PDP sun bayyana cewa zasu haɗa kan jam'iyyar su domin ceto Najeriya daga hannun gurbatacciyar gwamnatin APC a zaben 2023, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba da daddare, jim kaɗan bayan taron da suka gudanar a Abuja.

Yace taron wanda ya gudana a sirrince sun cimma nasara, inda suka tattauna kan gangamin taron PDP na ƙasa dake tafe.

Kara karanta wannan

Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Kan Mu Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Guardian ta ruwaito Tambuwal yace:

"Mun jima muna gudanar da taron, tun ƙarfe 3:00 na yamma, kuma sai da muka shafe awanni 7 muna tattaunawa."
"Mun gana da shugabannin PDP na jihohin da bamu da gwamna, mun tattauna da su kan yadda zamu kawo cigaba a cikin PDP, ba wai a babban gangami kaɗai ba, har zuwa gaba."
"Saboda PDP ta cigaba da samun nasara a Najeriya, kuma mu aike da sako mai kyau ga yan Najeriya cewa mun shirya, mun zama tsintsiya ɗaya."
"Kuma da izinin Allah zaɓen 2023 dake tafe, zamu haɗa karfi da karfe domin ceto Najeriya daga gurɓatacciyar gwamnatin jam'iyyar APC."

Waɗanne abubuwa aka tattauna a wurin taron?

Gwamna Tambuwal yace gwamnonin sun tattauna game da babban taron jam'iyyar PDP na ƙasa, wanda aka saka za'a gudanar ranar 20 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara

"Zaku ji matakan da zamu ɗauka kan gangamin a taron kwamitin zartarwa (NEC) da za'a yi gobe."

Kwamitin NEC na jam'iyyar PDP zai gudanar da taro ranar Alhamis domin tattauna kan rarraba manyan mukaman jam'iyyar zuwa yankunan kasar nan yayin da gangami na kasa ke kara kusantowa.

Zaɓen gwamnan Anambra

Da yake jawabi, Tambuwal yace gwamnoni da sauran shugabannin jam'iyya sun tattauna kan shirye-shiryen PDP a zaɓen gwamnan Anambra.

"Ɗan takarar mu a zaben Anambra ya samu halarta, kuma mun ji bayanai daga bakinsa kan shirye-shiryen PDP a Anambra, kuma muna tabbatar muku da cewa baki ɗayan mu kan mu a haɗe yake wajen goyon bayan jam'iyyar mu a Anambra."

A wani labarin kuma Rundunar yan sanda ta damke ƙasurgumin dan bindiga da wasu yan leken asiri da aama a Katsina

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isa, yace an cafke yan leken asirin yan bindiga a tsakanin bodar Katsina da Zamfara yayin da suke ɗauke da shanu 80 a wata babbar mota zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

SP Isah yace rundunar tana iya bakin kokarinta wajen yaki da ayyukan yan bindiga, satar shanu da sauran miyagun laifuka a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262