Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara
- Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya soke duk wani aiki ko tafiya da zata fitar da shi cikin jihar Zamfara
- Gwamnan yace zai zauna duk halin da ɗaukewar sabis zai jefa mutane shima ya shiga yanayin
- Ya kuma bayyana irin nasarorin da jami'an tsaro suka samu zuwa yanzun da irin matakan da ake cigaba da ɗauka
Zamfara - Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya soke duk wata tafiya da zata fitar da shi cikin jihar, dai dai lokacin da aka tsananta hare-hare kan yan bindiga, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
A makon da ya gabata ne hukumar sadarwa NCC ta umarci baki ɗaya kamfanonin sadarwa su datse sabis ɗinsu a jihar Zamfara.
Da yake zantawa da kafar watsa labarai ta DW Rediyo, gwamnan yace matakan da aka ɗauka kan yan bindiga ya fara haifar da ɗa mai ido.
Wane sakamako aka fara samu bayan ɗaukar matakai?
Matawalle ya bayyana cewa ɓarayi sun fara sako waɗanda suka sace don dole domin ba su iya ciyar da su saboda an toshe musu kafar samun abinci, man fetur da kuma sabis ɗin sadarwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace mutanen da suka shafe makwanni ko watanni a hannun yan bindiga yanzun sun dawo gida, yayin da suka fara zubar da abubuwan hawansu domin babu man fetur.
Wane matakai jami'an tsaro suka ɗauka a jihar?
A jawabin gwamnan yace:
"Shugaban rundunar sojojin ƙasa na cikin jihar mu domin jagorantar Operation ɗin jami'ansa. Sojoji da yan bijilanti sun shirya don kutsawa har maɓoyan yan bindiga a cikin jeji."
"Sojoji na cigaba da tsananta hare-haren, da yardar Allah sai an tarwatsa dukkan sansanonin yan ta'adda ɗaya bayan ɗaya, kuma muna samun nasara sosai."
Ba inda zanje - Matawalle
Gwamnan ya kara da cewa duk halin da al'ummar Zamfara suka tsinci kansu bayan datse sabis, shima zai ɗanɗani yanayin.
"Ba inda zanje, ina cikin Zamfara har zuwa sanda za'a kawo karshen wannan aikin. Nima zan ɗanɗani kuncin da datse sabis zai jefa mutanen Zamfara a ciki."
"Kamar yadda kuke gani, an jibge jami'an tsaro a wuraren bincike duk bayan kilomita biyar a faɗin jihar, domin ba zamu bar wani ɗan ta'adda ya tsira ba ko ya samu hanya."
A wani labarin kuma Ɓarayi Sun Sace Dalibai 1,409 a Najeriya Cikin Watanni 19, Miliyoyi Sun Salwanta Wajen Fansa
Wani sabon rahoto da ƙungiyar fasaha ta SBM ta fitar ya nuna cewa aƙalla ɗalibai 1,409 aka sace a faɗin Najeriya cikin watanni 19 da suka shuɗe.
Rahoton wanda akai wa take, "Sace ɗalibai daga makarantu a Najeriya," kungiyar ta bayyana adadin waɗanda hare-haren suka shafa tun daga watan Maris, 2020, zuwa yanzu.
Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya
Asali: Legit.ng