Gwarazan Yan Sanda Sun Damke Kasurgumin Dan Bindiga da Wasu Yan Leken Asiri da Dama a Katsina

Gwarazan Yan Sanda Sun Damke Kasurgumin Dan Bindiga da Wasu Yan Leken Asiri da Dama a Katsina

  • Gwarazan yan sanda sun samu nasarar kame masu kaiwa yan bindiga bayanan sirri a jihar Katsina
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, yace jami'ai sun cafke wani ƙasurgumin dan bindiga da aka jima ana nema
  • SP Isah yace rundunar tana iya bakin kokarinta wajen yaki da ayyukan yan bindiga, satar shanu da sauran miyagun laifuka a jihar

Katsina - Rundunar yan sandan Katsina ta cafke wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan yan bindiga da satar shanu, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Gwarazan yan sanda da suka fita sintiri kan hanyar Kankara-Sheme, karamar hukumar Dutsinma, sune suka kame mutanen.

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isa, yace an cafke yan leken asirin yan bindiga a tsakanin bodar Katsina da Zamfara yayin da suke ɗauke da shanu 80 a wata babbar mota zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta

Yan sanda sun kama yan leken asiri a Katsina
Gwarazan Yan Sanda Sun Damke Kasurgumin Dan Bindiga da Wasu Yan Leken Asiri da Dama a Katsina Hoto: channlestv.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa yan leken asirin mazauna garin Wanzamai ne, dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Yan sanda sun kama wani sanannen ɗan bindiga

Hakazalika, SP Isah ya kara da cewa an sake damke wasu yan leken asirin yan tada kayar baya biyu da kuma masu kaiwa yan bindiga man fetur yayin da yan sanda suka fita sintiri.

Sannan wani sanannen ɗan bindiga, Auwal Aliyu, ya shiga hannu yayin da yayi kokarin sajewa cikin yan bijilanti a ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

Kakakin yan sandan yace:

"Ɗan bindigan, mai kimanin shekaru 32, ya jima cikin jerin waɗanda ake nema ruwa a jallo a jihar saboda hannunsa a ayyukan yan bindiga da sace shanun mutane, sannan kuma yana taimaka wa yan ta'adda da bayanai."

Bugu da kari, SP Isah yace wannan nasarar kame shi da aka yi, na ɗaya daga cikin nasarorin da rundunar yan sanda ta samu a yakin da take da yan bindiga a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Cikin Sauki Sojoji Ke Maganin Yan Bindiga Tun Bayan Datse Sabis a Zamfara, Kwamishina

A wani labarin kuma kun ji cewa matar shugaban ƙasar Amurka na yanzu, Jill Biden, ta bar fadar white house, inda ta koma aikinta na koyarwa

Jill Biden, malamar koyar da rubutu ce tun mijinta Joe Biden, yana mataimakin shugaban ƙasa a zamanin mulkin Obama.

Jill ta zama mace ta farko, tana lamba ɗaya a Amurka sannan tana sana'arta ta koyarwa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel