Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

  • Jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ta yi sabbin mambobi yayin da 'yan APC 50,000 suka sauya sheka
  • Lamarin ya faru a ranar Asabar, inda dandazon mamobin da suka dawo PDP suka samu tarbar Atiku Abubakar
  • Sun bayyana manufarsu ta dawowa jam'iyyar PDP, inda suka ce sun yi hakan ne don ciyar da jihar gaba

Adamawa - Sama da mambobin jam’iyyar APC 50,000 ciki har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mista Kobis Ari Themnu, sun koma PDP a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya tarbe su a dandalin Ribadu Square na taro a Yola ya zarge su da yin imani da kuma daidaita amincin su ga jam'iyyar da ta gaza tun farko, inji rahoton jdairdar Leadership.

Kara karanta wannan

Kafa jam'iyyar APC shine babban kuskuren da aka taba yi a Najeriya, inji Atiku

Sai dai Atiku ya ce kuskuren su na kasancewa a cikin APC yanzu an gafarta musu, sannan ya kara tabbatar da cewa PDP ta shirya ta karbi mulkin kasar nan a zaben 2023.

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa
Jam'iyyar PDP | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya bukaci membobin wasu jam’iyyu da su shiga jam’iyyar PDP don ci gaban jihar da kasa baki daya.

Tun da farko, Gwamna Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa za a bai wa wadanda suka sauya sheka madafun da zasu taka rawa tare da tsoffin mambobin jam’iyyar don yin takara a kowane mukami.

Fintiri ya ba da tabbacin samar da babban taron PDP na gaskiya a jihar saboda babu bako a cikin jam'iyyar.

Ya bukaci sabbin membobin da su goyi bayan takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023.

Barista Tahir Shehu, shugaban PDP a jihar a cikin jawabinsa, ya ce bikin ya nuna farkon rushewar sauran jam’iyyun siyasa zuwa PDP saboda jam’iyyar ta himmatu wajen samar da shugaba na gaba daga yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati Tare da Wasu Mutum 50,000 Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

A jawabinsa yana cewa:

“Kofar jam’iyya a bude take ga sabbin mambobi saboda ayyukan raya kasa da gwamnatin yanzu ke bayarwa sun isa su yi magana da kan su tare da tantance alkiblar siyasa ga jihar a zaben 2023.
"Za mu yi aiki kafada da kafada da sabbin masu sauya sheka don ciyar da PDP gaba."

Kanal Andrawus Sawa wanda ya yi magana a madadin abokan aikinsa ya ce sun yanke shawarar shiga PDP ne saboda sun gamsu da tunanin jam’iyyar na inganta yanayin tsaro a kasar.

A cewarsa:

"Dalilin zuwan mu PDP shine hambarar da APC a matsayin jam’iyya a jihar."

Fitattu daga cikin wadanda suka sauya shekar sune Commodore Usman Sali Bodes (rtd), Daniel Bwala, Philip Gatuwa da Nedo Kufaltu.

Kafa jam'iyyar APC shine babban kuskuren da aka taba yi a Najeriya, inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin babban kuskuren Najeriya, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC

Atiku wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar 4 ga watan Satumba a garin Yola, jihar Adamawa yayin taro da manyan jiga-jigan APC suka koma PDP, ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da APC.

Ya yi kira ga membobin APC da su barranta da jam'iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin muguwar rawar da ta taka, yana mai cewa sauya sheka daga jam'iyyar ya nuna alamar karshen APC.

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ba da shawarar kirkiro da sabuwar rundunar 'yan sanda don kare makarantu daga hare-haren 'yan bindiga a yankunan da lamarin tsaro yake kara ta'azzara.

Ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani kan sace dalibai 73 da aka yi kwanan nan a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya dake Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Tsohon dan takarar shugaban kasan na jam'iyyar PDP ya kuma koka kan harin da sace daliban.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel