Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

  • Iyayen daliban makarantar da aka sace a Zamfara sun shiga damuwa bayan katse sabis a jihar
  • An sace dalibai 73 a wata makarantar gwamnati a makon jiya, lamarin da ya haifar da rudani
  • A halin yanzu iyaye sun ce basu ji ta bakin 'yan bindiga ba balle su san halin da 'ya'yansu ke ciki

Zamfara - Iyayen daliban da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun koka kan rashin iya jin ta bakin masu garkuwa da mutanen da suka sace 'ya'yansu.

Rundunar ‘yan sanda ta ce an sace dalibai 73 lokacin da 'yan bindiga suka mamaye makarantar da misalin karfe 11 na safiyar Laraba da ta gabata.

Dalibai biyar, dukkansu 'yan mata, sun tsere daga hannun 'yan bindigan ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse sabis
Taswirar jihar Zamfara | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa, a ranar Juma’a, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su katse sabis na sadarwa a Zamfara - lamarin da ya haifar da rashin sadarwar wayoyin salula a jihar.

Martanin iyaye game da katse sabis na layukan waya a jihar Zamfara

Da yake zantawa da TheCable a ranar Asabar, mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace, Idris Magaji, ya ce yana cikin duhu da damuwa game da matakan da ake dauka na kubutar da yaran da aka sace.

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse sabis
Malam Idris Magaji | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewar Magaji:

“A gaskiya ban yi farin ciki da wannan ba. Ban sani ba ko gwamnati na yin wani abu a kai domin ban ji ko ga komai ba."
"Idan gwamnati tana yin wani abu game da hakan, ya kamata su gaya mana (iyaye) cewa 'wannan shine matakin da muka dauka' don tabbatar da cewa an ceto yaran mu.

Kara karanta wannan

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

“Babu wata magana tsakanin mu iyaye, da gwamnati. Gwamnati ba ta ce mana komai ba. A gefen 'yan bindiga, ba su zo wurinmu ba don tattaunawa kan kudin fansa. Ya kamata gwamnati ta yi abin da ya dace don ceto yaranmu.”

A nasa bangaren, Bello Liman, mahaifin da 'ya'yansa biyu ke hannun 'yan bindiga, ya tabbatar da abin da Magaji ya fada tare da fatan hukumomi za su kubutar da wadanda aka sace.

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse sabis
Malam Bello Liman | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A kalaman Liman:

"Ina jin ciwo sosai. Lokacin da aka yi satar ina Gusau. Ina tunanin gwamnati na iyakacin kokarinta don kubutar da yarana. Ina da imani cewa da yardar Allah za a kubutar da su."

Suweba Mohammed, daya daga cikin daliban da suka tsere, tun da farko ya shaidawa TheCable cewa 'yan bindigan sun basu abinci a tafin hannayensu kuma sun basu ruwa gora guda daya dukkaninsu su sha.

Rikicin Jos: El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara

A wani labarin, Samaila Dahiru, dalibin da ya tsere daga hannun 'yan bindigan shi ma ya ba da labarin abin da ya faru bayan an sallame shi daga asibiti inda aka yi masa jinyar harbin bindiga.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da takwaransa na jihar Filato, Simon Bako Lalong, sun yi alkawarin hada kai da rundunar Operation Safe Haven (OPSH) da sauran hukumomin tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar jihohin biyu.

Sun yi wannan alkawari ne ranar Lahadi 5 ga watan Satumba lokacin da El-Rufai ya ziyarci Lalong don jajantawa gwamnati da mutanen jihar Filato kan hare-hare da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna El-Rufai ya ce:

“Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba. Muna da dangantaka mai karfi kuma tun lokacin da muka hau mulki a 2015, ni da Gwamna Lalong muna tuntubar juna; Gwamna Lalong ne ya gabatar da mu ga Cibiyar Tattaunawar Ba da Agaji, wata kungiya mai zaman kanta ta duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 Daga Hannun Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel