Matasan Arewa sun nemi Obansajo, IBB su taimaka a samo mafita ga matsalolin Najeriya

Matasan Arewa sun nemi Obansajo, IBB su taimaka a samo mafita ga matsalolin Najeriya

  • Kungiyar shugaban matasan Arewa sun bukaci Obasanjo ya nemo mafita ga 'yan Najeriya
  • Kungiyar ta bukaci shugaban da ya yi kira ga taron iyayen kasa domin samar da mafita ga kasar
  • Sun kuma bukaci ya ayyana PDP a matsayin jam'iyyar da za ta iya kawo mafita ga 'yan kasar

Abeokuta, Ogun - Kungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF), wata kungiyar gamayyar kungiyoyin Arewa 42, ta yi kira ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya gaggauta kiran taron “Iyayen Najeriya” da nufin shiga tsakani a matsalolin kasar da kuma samar da mafita.

Kungiyar musamman ta yi kira ga Obasanjo da ya shiga tsakani a rikicin da ke kara ta'azzara a jam'iyyar PDP, tare da bayyana cewa jam'iyyar ita ce kadai fata ga 'yan Najeriya, Sun News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wata kotu ta hana Secondus ya ci gaba da zama a matsayin shugaban PDP na kasa

Ta kuma bayyana Obasanjo a matsayin "gogaggen dan kasa wanda ya yi imani da gamayyar Najeriya."

Shugaban NYLF na kasa, Elliot Afiyo, ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abeokuta, jihar Ogun, jiya, jim kadan bayan ganawarsa da Obasanjo.

Matsalolin Najeriya: Matasan Arewarewa sun nemi IBB, Obansajo su taimaka a samo mafita
Tambarin Arewa | Hoto: hausa.leadership.ng

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Afiyo, wanda ya ambaci wasu 'Iyayen Najeriya' da suka hada da tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya), Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya) da Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da Ernest Shonekan.

Kungiyar ta lissafo matasalolin Najeriya da suka gada da 'yan bindiga, yawan garkuwa da mutane, cin hanci da rashawa, barakar tattalin arziki, tashe-tashen hankula daga 'yan aware da dai sauran matsalolin da sauka dabaibaye kasar.

Ya ce lokaci ya yi da wadannan “‘yan Najeriya masu kishin kasa” za su hadu su kuma samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta kafin su dulmuye kasar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

Shugaba Buhari ya kasa cika burin 'yan Najeriya

Ya bayyana cewa NYLF tana cikin kungiyoyin da suka marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a 2015, amma yayi nadamar cewa shugaban kasar ya kasa cika burin ‘yan Najeriya.

Ya zargi APC da rashin kwarewa a siyasa wajen magance dubban kalubalen da ke fuskantar kasar.

A cewarsa, PDP ce kadai za ta iya samar da wata madaidaiciyar mafita kuma ta kafa ingantaccen shugabanci da 'yan Najeriya ke fata nan gaba.

Musabbabin rikicin da ya dabaibaye PDP

Ya ce rikicin da ya dabaibaye PDP ya samo asali ne sakamakon nuna ikon mulki tsakanin wasu gwamnoni saboda burinsu na shugabancin kasa a 2023.

Da yake magana kan barakar neman canjin mulki kafin shekarar 2023, Afiyo ya ce shugaban na gaba zai iya fitowa daga kowane bangare na kasar, muddin dan takarar yana da cancanta da karfin da zai magance matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koma makaranta

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa domin su dinke baraka

A wani labarin, Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, wacce ta kunshi gwamnonin jihohi 13, za ta yi taro a yau a Abuja don tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi kungiyar ta siyasa, The Guardian ta ruwaito.

Wata sanarwa, a jiya Laraba 25 ga watan Agusta ta hannun Darakta Janar na kungiyar, C.I.D Maduabum, ta yi bayanin cewa shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, bayan tattaunawa da abokan aikinsa sun amince da kiran taron.

A cewar Nigerian Tribune, Maduabum ya ce Tambuwal ya kira taron ne tare da abokan aikinsa, inda ya tabbatar da cewa "za a tattauna abubuwan da suka faru a PDP."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel