Da dumi-dumi: Wata kotu ta hana Secondus ya ci gaba da zama a matsayin shugaban PDP na kasa
- Saboda wasu dalilai da dama, ana iya kiran shekarar 2021a matsayin mafi muni ga Prince Uche Secondus, shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa
- Shahararren dan siyasar na kudu maso gabas na ta yawo daga shari’ar wannan kotu zuwa wancan a cikin kankanin lokaci
- Bayan komawarsa kan kujerarsa, wata kotu a Kuros Riba ta bayar da umarni a ranar Juma’a, 27 ga watan Agusta, inda ta hana Secondus gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar
Kuros Riba - A cikin makwanni biyu, Prince Uche Secondus, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, ya samu umarni da yawa daga manyan kotuna game da kujerarsa.
Umarnin baya-bayan nan daga babban kotun jihar Kuros Riba ne wacce a ranar Juma’a, 27 ga watan Agusta, ta hana Secondus sake komawa matsayin shugaban jam’iyyar, The Cable ta ruwaito.
Wannan umurnin, wanda alkalin kotun, Mai shari’a Edem Kooffreh ya karanta ya zo ne bayan da Enang Wani ya shigar da kara.
A cikin karar, Wani, wanda ya ambaci Secondus a matsayin wanda ake kara na farko, ya roki kotun da ta dakatar da shi daga jagorantar taron kwamitin zartarwa na kasa da aka shirya yi a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta.
Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP
A baya mun kawo cewa wata babbar kotu a jihar Kebbi ta bada umarnin cewa Prince Uche Secondus ya koma matsayinsa na shugaban jam'iyyar PDP na kasa.
Alkalin kotun, Mai shari'a Nusrat Umar, ita ce ta bada wannan umarnin bayan shigar da kara gabanta a Birnin Kebbi, babbar birnin jihar.
A karar da aka shigar gaban kotun, wadda akaiwa lamba KB/AC/M. 170/2021, mai shari'a Nusrat tace ta gamsu sosai bayan karanta rantsuwar wanda ake karewa.
Asali: Legit.ng