Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

  • An kashe mambobin IPOB/ESN da yawa a karamar hukumar Oru ta gabas ta Imo a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta
  • An kashe masu laifin ne a artabun da suka yi da sojoji na musamman da tawagar rundunar 'yan sanda a jihar
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Michael Abattam ne ya tabbatar da hakan

Jihar Imo - A yayin wani artabu a karamar hukumar Oru ta gabas ta jihar Imo a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta, ‘yan sanda sun yi nasarar kashe shugaban‘ yan asalin yankin Biyafara (IPOB) da Kungiyar Tsaron Gabas (ESN).

Jaridar PM News ta ruwaito cewa a yayin samamen, jaruman jami'an sun kwato Na'urorin fashewa guda uku (I.E.D), bindigogi, bindigar gargajiya guda daya tare da wata mota kirar Toyota Highlander SUV.

Da dumi-dumi: ‘yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas
‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Sai dai mai magana da yawun rundunar, CSP Michael Abattam, ya ce yayin da suke dawowa daga aikin da ya yi nasara, membobin kungiyoyin da aka haramta sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna inda suka yi artabu da su wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla dan sanda daya da masu laifi da dama.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa domin su dinke baraka

A lokacin musayar, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Rabiu, ya aika da runduna ta musamman da tawagar dabaru karkashin jagorancin ACP Evans Shem.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

A wani labari, jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) tare da hadin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro sun cafke wata budurwa yar shekara 22 mai suna Gloria Okolie.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwar da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Aremu Adeniran, ya fitar kuma Legit.ng Hausa ta samu a ranar Lahadi, 22 ga watan Agusta.

Adeniran ya lura cewa an kama Okolie ne saboda hada kai da ta yi a cikin jerin hare-haren da aka kai da gangan kan jami'an tsaro, wasu muhimman wurarenmallakin kasa ciki har da ofisoshin INEC da kashe jami'an tsaro a yankin kudu maso gabashin kasar.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Asali: Legit.ng

Online view pixel