Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa domin su dinke baraka

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa domin su dinke baraka

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun yi kiran taron gaggawa don magance matsalar jam'iyyarsu
  • Shugaban kungiyar gwamonin ya sanar da haka a jiya Laraba 25 ga watan Agustan 2021
  • Taron, inji majiyoyi zai kawo karshen tabarbarewar shugabanci da aka samu a jam'iyyar

Abuja - Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, wacce ta kunshi gwamnonin jihohi 13, za ta yi taro a yau a Abuja don tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi kungiyar ta siyasa, The Guardian ta ruwaito.

Wata sanarwa, a jiya Laraba 25 ga watan Agusta ta hannun Darakta Janar na kungiyar, C.I.D Maduabum, ta yi bayanin cewa shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, bayan tattaunawa da abokan aikinsa sun amince da kiran taron.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matakin da Ta Dauka Bayan Kotu Ta Dakatar da Secondus

A cewar Nigerian Tribune, Maduabum ya ce Tambuwal ya kira taron ne tare da abokan aikinsa, inda ya tabbatar da cewa "za a tattauna abubuwan da suka faru a PDP."

Rikicin PDP: Gwamnonin PDP za su yi taron gaggawa a yau Alhamis
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce gwamnoni sun umarci dukkan membobin PDP da masu ruwa da tsaki da su yi hakuri yayin da ake kokarin tabbatar da ci gaba da wanzar da kwanciyar hankali a jam'iyyar a cikin kwanaki masu zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Takaitaccen bayanin sanarwar ya ce:

“Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, bayan tuntubar abokan aikinsa ya kira taron gaggawa na kungiyar a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021 da karfe 5:00 na yamma. Taron zai tattauna abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a PDP."

Manufar yin taron

Majiyoyi sun yi nuni da cewa taron ya zama wajibi don gaggauta warware rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da tsohon sanatan Najeriya ya mutu

Taron zai yanke hukunci na karshe kan lokacin da za a gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Suleiman Nazif, a ranar Talata ya sanar da cewa za a gudanar da taron na NEC a gobe Juma'a.

"Rashin nasarar da Shugaban Jam'iyyar na kasa, Prince Uche Secondus da aka dakatar ya yi na kiran taron NEC na daya daga cikin batutuwan da suka sa lamarin ya tabarbare."

Atiku ya tura sako ga PDP, ya ce duk rintsi a kwace mulki a hannun Buhari a 2023

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya aika sako ga shugabancin jam'iyyar PDP gabanin zaben shugaban kasa mai zuwa a kasar a shekarar 2023.

Takardar an ce bayyana alama ce ta farko na sake nuna sha’awar Atiku Abubakar na neman tikitin takarar shugaban kasa na 2023 na jam’iyyar adawar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Atiku, bai bayyana ko zai nemi wani matsayi a yakin neman zaben shugaban kasa ba a cikin sakon mai kwanan wata 29 ga Yuni, 2021 ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.