Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koma makaranta

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koma makaranta

  • Biyo bayan jita-jitan cewa Atiku ya koma Dubai da zama, dan siyasan ya yi martani
  • Tsohon mataimakin shugaban kasan yace makaranta ya koma karo ilimi
  • Ya ce Obasanjo ne ya bashi shawaran komawa makaranta

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da yasa ya dade ba ya Najeriya.

Rahotanni sun yadu cewa tsohon mataimakin shugaban kasan ya arce daga Najeriya tun bayan da ya sha kashi a zaben shugaban kasa a 2019.

Atiku ya bayyana cewa ya koma karatun digirinsa na biyu ne kan ilmin alaka tsakanin kasashe a jami'ar Cambridge dake kasar Birtaniya.

Atiku ya bayyana hakan ne bayan zaman majalisar dattawan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, ranar Alhamis, a Wadata Plaza, birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Yace:

"Mutane da yawa na tambayan cewa ina naje tun Satumba, kuma abin ya fara haifar jita-jita tsakanin mutane."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina mai cewa na koma makaranta ne domin karasa lakca a Mayu, saboda ina karatun digiri na biyu a Alakokin kasashe a jami'ar Cambridge."
"Ina son amfani da wannan dama wajen godewa tsohon shugaba Obasanjo da ya bani shawaran zuwa jami'ar don karatu."

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koma makaranta
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koma makaranta

Rikicin PDP ya kare, Atiku

Atiku ya kara da cewa rikicin dake cikin jam'iyyar PDP yazo karshe, kuma zasu lashe zabe a 2023.

"Na yi imanin PDP za ta cika burikan mutanen Najeriya saboda sun san mu fiye da kowace jam'iyya."

"Masu farin cikin cewa an samu baraka cikin PDP, yanzu ban sani ko zasu koma ba saboda an dinke barakar."

Ba mu buƙatar Atiku, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A bangare guda, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel