'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

  • Rahoto daga jihar Zamfara na tabbatar da cewa, an sako daliban da aka sace a kwalejin noma ta Bakura
  • An ruwaito cewa, gobe Juma'a za a kai daliban da malamansu da aka sako zuwa fadar gwamnatin jihar
  • An sace daliban ne kwanakin baya, lamarin da ya kai ga dakatar da zaman majalisar dokokin jihar

Zamfara - An sako malaman makaranta da daliban kwalejin aikin gona da kimiyyar dabbobi ta jihar Zamfara dake Bakura.

Wata majiya daga tushe na kusa da gwamnatin jihar Zamfara da ta nemi a sakaya sunanta ta sanar wa jaridar Punch cewa za a kawo su gidan gwamnati gobe Juma'a 27 ga watan Agusta, amma, ya ki yin karin bayani.

Idan za a iya tunawa a ranar 16 ga watan Agusta, 2021 wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari kwalejin tare da sace mutane 19 da suka hada da ma'aikata uku, dalibai 15 da direba.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Jihar Kaduna ta kwashe dalibai 'yan jiharta dake karatu a jihar Filato

An kashe mutane hudu yayin da 'yan bindigan suka yi awon gaba da dalibai da malamai na makarantar.

Da dumi-dumi: An sako daliban kwalejin noma da aka sace a jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa yan bindigan sun kai hari kwalejin aikin gona ta Zamfara dake karamar hukumar Bakura a ranar Lahadi lokacin da lamarin ya faru.

Mataimakin magatakardar kwalejin, Atiku Aliyu Bakura, ya tabbatar da sace mutanen.

An ruwaito Bakura yana cewa mutane hudu da suka hada da dan sanda da masu gadi uku sun mutu a harin.

An dakatar da zaman majalisa a Zamfara saboda sace mahaifin kakakin majalisar

Majalisar Jihar Zamfara ta dakatar da zamanta har sai baba ta gani saboda sace mahaifin kakakin majalisar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Makonni uku da suka gabata ne yan bindiga suka sace mahaifin kakakin majalisar bayan kai hari a garinsu na Magarya a yankin Kanwa na karamar hukumar Zurmi.

Kara karanta wannan

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

Mahaifin kakakin majalisar da aka sace, Alhaji Mua'azu Abubakar shine hakimin Sabon Garon Magarya a yankin Kanwa a karamar hukumar.

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma. A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel