Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

  • Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari Islamiyya a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina
  • Yan bindigan sun sace dalibai da dama sannan sun yi awon gaba da malamin makarantar islamiyya guda daya
  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ta bakin kakakinta SP Gamba Isah ta ce ba za ta iya tabbatar da harin ba a yanzu

Faskari, Jihar Katsina - Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina
Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zamu kashesu cikin awa 24 idan ba'a biyamu ba, Yan bindigan da suka sace dalibai a Zamfara sun saki bidiyo

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba.

Ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Yan bindiga sun halaka mutane uku a Batsari

Kazalika, an kashe mutane uku a yayin da yan bindiga suka kai hari a garin Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.

Wani mazaunin Batsari ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa daya daga cikin wadanda abin ya shafa wacce gwagwansa ce ta rasu sakamakon buguwar zuciya saboda tsoron harbin bindigan yan fashin dajin.

Ya kuma ce sauran mutane biyun sun mutu ne sakamakon harsashi da ya ratsa jikinsu

Ya ce:

"A lokacin da yan bindigan suka taho Batsari, mun gano cewa jami'an tsaro suna can kauyen Dankar inda yan bindigan suka musu kawanya."

Ya kara da cewa an sace mutum takwas yayin harin na Batsari.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce zai tuntubi DPO na Batsari domin sannin tabbas kafin ya yi tsokaci a kan harin na Faskari domin sojoji ke kula da garin.

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labari daban, hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel