Rikicin Jos: Jihar Kaduna ta kwashe dalibai 'yan jiharta dake karatu a jihar Filato
- Duba da yadda rikici a Jos yake kara ta'azzara, gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe dalibai 'yan asalin jihar Kaduna a Filato
- Wannan na zuwa ne bayan barkewar rikici a 'yan kwanakin nan, lamarin da ya kai ga sanya dokar hana fita a wasu sassan jihar
- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa, wannan wani yunkuri ne na kubutar da daliban daga fadawa rikicin dake faruwa
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta ta sanar da kwashe ‘yan asalin jihar wadanda daliban jami’ar Jos ne da sauran manyan makarantun jihar Filato, Punch ta ruwaito.
Wannan ya biyo bayan yawaitar kashe-kashe a garin Jos ta Jihar Filato da sake sanya dokar hana fita a wasu sassan jihar.
Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu da bashi na jihar Kaduna, Malam Hassan Rilwan, wanda ya sanar da hakan, ya ce an kammala kwashe daliban a karshen makon da ya gabata.
Ci gaban, in ji shi, ya yi daidai da umarnin gwamnatin jihar cewa ya kamata a kwashe dukkan daliban jihar Kaduna da suka makale saboda yanayin tsaro a jihar Filato.
A cewarsa, Jami’an tsaro karkashin kulawar hukumar sun kwashe dalibai 87 a ranar Juma’a, 20 ga Agusta, 2021, inda ya kara da cewa tuni aka sake sada daliban da danginsu.
Rilwan ya ce Hukumar za ta ci gaba da kasancewa cikin kwazo a cikin irin wannan yanayi mai rikitarwa tare da bai wa ‘yan kasa tabbacin jajircewar gwamnati na kare rayukan daliban jihar a Jihar Filato da sauran wurare.
Rilwan ya kara da cewa:
"Hukumar ta kuma lura da goyon bayan da ta samu daga Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Uba Sani wanda ya taimaka matuka wajen kwaso daliban."
Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe
Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.
Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos
A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.
Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.
Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.
Asali: Legit.ng