Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, gwamna Ortom na Benue ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama
  • Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana hakan a yau Laraba cikin wata sanarwa
  • Gwamnati ta zarge shi da tunzura wata kabila wajen hallaka wata kabilar, wanda ya jawo mace-mace da dama

Abuja - Fadar shugaban kasa ta zargi gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da kunna wutar kiyayya tsakanin mazauna a jiharsa ta hanyar kai hari kan wata kabila wanda ya zama daidai da kisan kare dangin da ya taba faruwa a Rwanda.

Babban mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Laraba, 25 ga watan Agusta ta shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Babu mamaki ‘Yan bindiga sun aukawa NDA ne da nufin a bata wa Buhari suna

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama
Garba Shehu | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Shehu ya ce kamar yadda ya faru a Rwanda inda shugabannin Hutu na wancan lokacin suka tunzura ‘yan kasarsu a kan junansu, inda suka ce akwai "boyayyar manufar Tutsi” kan Hutu, Ortom ma haka ya ce akwai "boyayyar manufar Fulani” kan sauran kabilun jiharsa da kasar.

A cewar Garba Shehu:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamna Samuel Ortom na da karancin sanin ka’idojin siyasa. Za mu iya ganin haka daga yadda ya canza jam’iyyarsa sau biyar a lokacin da bai yi fice ba.
“Duk lokacin da ya ji guguwar canji na kadawa ta wata hanya, sai ya bi ta.
“Abin takaicin shine, ga mutanen kirki na jihar Benue, shine mawuyaciyar alkiblar da yake kadasu a yau itace na bangaranci da kabilanci.
"A wani yunkuri na hakaka siyasarsa, Ortom na daukar hanya mafi arha kuma mafi kaskanci ta hanyar wasa da kabilanci - kuma yin hakan da gangan ya jawo mutuwar 'yan Najeriya marasa laifi ta hanyar tunzura manoma akan makiyaya, da Kiristoci akan Musulmai.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Mutanen Benue basu cancanci irin wannan gwamnan ba

A cewar Garba Shehu, al'ummar jihar Benue bai kamata ace suna da irin wannan shugaba ba, kuma yana addu'ar Allah ya kawo zabe na gaba su hambarar da gwamnatinsa.

A kalamansa, Shehu yace:

“Wadannan ba ayyukan mutum bane da ya kamata a amince da shi wajen gudanar da ayyukan gwamnati ko rike mukamin gwamnati.
“A ce gwamnan wata babbar jiha a Najeriya ya nuna kiyayya ta kabilanci a siyasance, tabo ne ga kasarmu. Mutanen kirki, kuma masu adalci a jihar Benue sun cancanci fiye da wannan, kuma muna dokin zuwan zabe lokacin da za su sami damar maido da martabar ta.”

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin soji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa ya tada Lauyoyi, yana maganar shigar da Shugaba Buhari gaban kotu

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

"Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel