Gwamnan PDP a Arewa ya tada Lauyoyi, yana maganar shigar da Shugaba Buhari gaban kotu
- Gwamnan Samuel Ortom ba ya goyon bayan dawo da labobin kiwon dabbobi
- Ortom yace zai tafi kotu idan dai Gwamnatin Tarayya ba ta canza shawara ba
- Gwamnan ya nemi na-kusa da Shugaban Najeriya, su zauna su ja hankalinsa
Benue - A ranar Lahadi, 22 ga watan Agusta, 2021, gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom yace zai iya shiga kotu da mai girma shugaba Muhammadu Buhari.
Wani mataki gwamnatin Benuwai za ta dauka?
Jaridar Punch ta rahoto gwamna Samuel Ortom yana cewa zai kai shugaban Najeriya kotu idan ya hakikance a kan dawo da labobin kiwon dabbobi a Najeriya.
Samuel Ortom ya fito ya na sukar matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na farfado da labobi, gwamnan yana cewa hakan ya saba kundin tsarin mulkin kasa.
Da aka tuntubi gwamnan na Benuwai a kan wannan batu, sai yace jiharsa ba za ta amince da wannan shiri ba, ya yi barazanar kai karar gwamnatin tarayya kotu.
“Har na fadakar da Lauyoyina su fara shirye-shirye. Zan kalubalance wannan a kotu, kuma ina sa ran cewa shari’a za ta ba ni gaskiya.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Maganar gaskiya idan mutanen kasa sun amince da killace dabbobi, meyasa shugaban kasa yake dage wa a kan a cigaba da kiwo a fili.”
Filaye ba su isa mutane ba - Ortom
Gwamna Samuel Ortom yace babu wani fili da aka yi tanadi a yau domin dabbobi su rika kiwo a fili. Jaridar Cable tace kungiyar Afenifere ta na tare da gwamnan.
“A shekarun 1950s da aka kawo wannan tsari, mutane nawa ne a Najeriya; ba a kai miliyan 40 ba. Yanzu mun haura mutum miliyan 200.”
A cewar Ortom, filin da ake da shi a Najeriya, ya yi wa jama’a kadan, don haka babu dalilin a samar da hanyoyi na musamman da dabbobi za su rika yin kiwo.
“Shugaban kasa ya na da hadimai; lauyan gwamnati, Abubakar Malami, da sauran lauyoyin da suke tare da shi, su ba shi shawara. Ni ba zan yadda da hakan ba."
Kwanaki kun ji cewa ana rokon gwamnatoci su fara gyaran hanyar garin Magama zuwa Saminka, hanyar za ta taimaka wajen gujewa bi hanyar Jos mai hadari.
Kamar yadda wani malami ya bayyana, idan aka iya kammala gyara titin Saminka zuwa Magama, an huta da shiga Filato, inda miyagu suke kashe Bayin Allah.
Asali: Legit.ng