Garba Shehu: Babu mamaki ‘Yan bindiga sun aukawa NDA ne da nufin a bata wa Buhari suna
- Fadar Shugaban kasa ta yi magana game da abin da ya faru a makarantar NDA
- Garba Shehu yana ganin kamar ‘Yan siyasa na neman bata sunan Gwamnati ne
- Hadimin Shugaban kasar ya na mamakin abin da ya faru a irin wannan lokacin
Abuja - Hadimin shugaban Najeriya, Garba Shehu, yace harin da aka kai a makarantar sojoji na iya zama shiri da nufin bata sunan shugaba Muhammadu Buhari.
Garba Shehu ya yi magana
Malam Garba Shehu ya yi wannan magana ne a lokacin da ‘yan jarida su ka yi hira da shi a gidan talabijin Channels TV a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta, 2021.
Mai magana da yawun shugaban kasar yace Mai girma Muhammadu Buhari yana sa rai sojoji su bincika, su gano ainihin abin da ya faru, a shaida wa Duniya.
Jaridar The Cable ta rahoto Garba Shehu yana bayyana aukuwar wannan lamari da abin takaici da Allah-wadai, sannan yace ba zai rasa burbushin siyasa ba.
Shehu yake cewa akwai yiwuwar an kitsa wannan danyen aiki domin a ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta ji kunya a lokacin da ake samun nasarori.
A cewar Shehu wannan abin ya faru ne a tsakiyar lokacin da jami’an tsaro suke samun galaba a kan ‘yan ta’adda da ‘yan bindigan da ke tada kayar baya a kasar.
Siyasa ce ko ta'addanci?
“Siyasa ce? Wani yana so ya jawo wa gwamnati abin kunya da wannan ne?"
“Shugaban kasa bai ji dadin abin ba, ya yi tir da lamarin. Yanzu ya rage wa mahukuntan sojoji suyi bincike da kyau, su bayyana abin da ya wakana.”
Hadimin shugaban kasar ya duba lamarin ta fuskoki dabam-dabam; ko tsantsagwaron laifi aka shirya domin a nuna wa sojoji ba su isa ba, ko akwai siyasa a ciki.
"A harkar siyasa – inda mutane suke neman samun farin jini da irin wannan abin takaici, ba za ka ce babu siyasa a lamarin ba, komai ma ya na iya faru wa.”
Fadar shugaban kasa ta ce za a iya hana aukuwar harin, sannan ta yi wa iyalan sojojin da aka rasa ta’aziyya
Ya aka yi 'Yan bindiga suka shiga NDA
An samu labari barci ya ci karfin sojojin da aka tanada a dakin CCTV a lokacin da abin ya faru Hakan ya sa ‘Yan bindiga su ka shiga makarantar sojojin, suka yi ta’adi.
Rahotanni sun ce idan hakan ta tabbata, za a hukunta sojojin da barci ya dauke a bakin aiki. Daga baya an ji cewa hedikwatar tsaro ta kasa ta musanya wannan rahoton.
Asali: Legit.ng