Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani kan harin da 'yan bindiga suka kai NDA
  • Ya ce, wannan ya kamata ya zama izina, ya kuma zama sanadin da zai sa a kara kaimi wajen yakar 'yan bindiga
  • Ya kuma ce, 'yan ta'adda na ci gaba da fuskantar fushin jami'an sojojin Najeriya, don haka dole a dage

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin soji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar.

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

"Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya yi martani mai zafi kan harin da aka kai NDA
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu taimaka masa a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya ce, shugaban ya lura cewa mugun nufin da masu aikata laifuka ke yi don rage martabar sojojin kasar a idon duniya ya gaza.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da sojoji ke ragargazar masu tayar da kayar baya, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran ire-iren masu aikata miyagun laifuka, musamman a arewa maso gabas.

Ya kamata 'yan Najeriya su ke yabawa sojojin Najeriya

A bangare guda na sanarwar, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, duba da namijin aikin sojojin Najeriya ke yi ya kamata 'yan Najeriya suke yaba musu, hakanan ya godewa 'yan Najeriyan da ke yabawa sojoji.

Adesina a cikin sanarwar yana cewa:

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

"Shugaban ya gode wa dukkan 'yan Najeriya da ke darajawa da yaba kokarin sojojinmu, kuma yana kira ga wadanda ke sa siyasar kiyayya a lamarin tare da munanan ayyuka da su guji hakan, lura cewa maimakon adawa, wannan lokaci ne ga duk masu kishin kasa da mutanen da ke da niyyar tallafawa su karfafawa dakaru a fagen daga."

Rundunar soja ta karyata zarginta da ake da son maida tubabbun Boko Haram sojoji

A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta ce ba za ta dauki tsoffin 'yan ta'adda masu tayar da kayar baya a cikin rundunar sojojin Najeriya ba, The Cable ta ruwaito.

Kakakin rundunar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata 24 ga watan Agusta a babban birnin tarayya Abuja.

Nwachukwu ya ce hankalin sojoji ya je ga wani bidiyo da wani matashi ya watsa a kafafen sada zumunta kuma Anthony Jay ya shirya wanda ya danganta rugujewar sojojin Afghanistan da mika wuya ga mayakan Boko Haram a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Asali: Legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel