Ba Gudu Ba Ja da Baya, Kungiyar Likitoci NARD Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu

Ba Gudu Ba Ja da Baya, Kungiyar Likitoci NARD Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu

  • Kungiyar Likitoci NARD tace sam bata san da cigaba da zaman kotu ranar Litinin ba
  • Shugaban kungiyar, Uyilawa Okhuaihesuyi, yace kungiyar ta ga rahoton zaman a shafukan jaridu
  • Shugaban ya kara da cewa yajin aikin su na nan ba gudu babu ja da baya har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu

Abuja - Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta maida martani kan hukuncin kotun ma'aikata "mai rikitarwa" na ranar Litinin.

Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa kotun dake zamanta a Abuja ta umarci ɓangarori biyu, gwamnati da NARD, su jingine duk wani rashin jituwa su rungumi sulhu.

Da yake zantawa ta wayar salula da wakilin Premium times, shugaban kungiyar NARD, Uyilawa Okhuaihesuyi, yace kungiyarsu ta ga labarin zaman kotun ne a shafukan jaridu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: FG Ta Yi Nasara, Kotu Ta Umarci Likitoci Su Janye Yajin Aiki

Likitoci sun cigaba da yajin aiki
Ba Gudu Ba Ja da Baya, Kungiyar Likitoci NARD Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Bamu san da zaman kotu ba

Okhuaihesuyi yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bamu san an yi wani zama ba, mun ji labarin ne a kafafen watsa labarai kuma shiyasa ma bamu halarci zaman kotun ba."

Yace abinda kungiyarsu take da masaniya shine an ɗage sauraron shari'ar har zuwa 15 ga watan Satumba.

Yajin aiki ba gudu ba ja da baya

Mista Okhuaihesuyi ya musanta jita-jitar cewa kotu ta umarci likitocin su janye yajin aiki kuma su koma bakin aiki.

Yace yajin aiki ba gudu ba ja da baya har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu.

Wane umarni kotu ta bayar?

Sabanin rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka buga, Premium times ta ruwaito cewa mai shari'a, John Targema, ya yi fatali da bukatar dakatar da likitocin daga yajin aikin da suke.

Wannan shine karo na biyu da alkalin ya yi fatali da makamanciyar wannan bukatar.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wani labarin kuma Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotu Na Dakatar da Shi Daga Mukaminsa

Secondus yace matukar an shigar da kararsa kotu to ya kamata ace yasani kuma an bashi damar kare kansa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Secondus ya yi zargin cewa labarin dakatar da shi ya fito ne daga ofishin na kusa da gwamnan jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel