Da Dumi-Dumi: FG Ta Yi Nasara, Kotu Ta Umarci Likitoci Su Janye Yajin Aiki Su Koma Bakin Aiki

Da Dumi-Dumi: FG Ta Yi Nasara, Kotu Ta Umarci Likitoci Su Janye Yajin Aiki Su Koma Bakin Aiki

  • Kotun ma'aikata ta kasa dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, umarci NARD ta dakatar da yajin aikin da take
  • Alkalin kotun, Mai shari'a John Targema, shine ya bayyana haka yayin da yake yanke hukunci kan bukatar masu shigar da kara
  • Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta tsunduma yajin aiki ranar 1 ga watan Agusta bisa wasu dalilai

Abuja - Kotun ma'aikata ta kasa dake zamanta a Abuja (NIC) ta umarci kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta janye yajin aiki, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Sai dai Alkalin kotun, Mai Shari'a John Targema ya umarci dukkan ɓangarorin biyu, gwamnati da NARD, su warware rashin jituwar dake tsakaninsu, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga

Punch ta ruwaito cewa Likitocin sun tsunduma yajin aiki a ranar 1 ga watan Agusta kan rashin biyansu albashi yadda ya kamata da sauran wasu dalilai.

Kotu ta umarci NARD ta janye yajin aiki
Da Dumi-Dumi: FG Ta Yi Nasara, Kotu Ta Umarci Likitoci Su Janye Yajin Aiki Su Koma Bakin Aiki Hoto: af24news.com
Asali: UGC

Alkalin kotun yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan duba da kuma nazari kan rantsuwa da kuma bukatar gaggawa da masu shigar kara suka gabatar. Kotu ta auna kuma ta yi biyayya ga dokoki kamar yadda aka gabatar mata."
"Ina bada umarnin cewa a dakatar da duk wata rashin jituwa tsakanin mai shigar da kara da kuma waɗanda ake kara yayin da za'a cigaba da sauraron shari'ar har zuwa karshe."

Kotu ta ɗage sauraron karar har zuwa Satumba

Alkalin ya kara bada umarni ga waɗanda ake kara su tabbatar sun dauki mataki game da hukuncin da aka yanke kafin zama na gaba.

Daganan kuma sai alkalin kotun, mai shari'a John Targema, ya ɗage zaman sauraron karar zuwa 15 ga watan Satumba, inda za'a cigaba da shari'a kan sauran abubuwan da aka shigar a gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

A wani labarin kuma Dakarun Sojoji Sun Fafata da Yan Bindiga Sun Kubutar da Matafiya a Kaduna

Dakarun sojin Operation Safe Haven sun kubutar da wasu matafiya 15 da yan bindiga suka sace a Jagindi, karamar hukumar Jema'a, jihar Kaduna ranar Lahadi.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace sojojin sun kai ɗauki ne bayan wani kiran gaggawa da aka musu kan lamarin sace matafiyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel