Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotu Na Dakatar da Shi Daga Mukaminsa

Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotu Na Dakatar da Shi Daga Mukaminsa

  • Shugaban PDP, Uche Secondus, yace idan dagaske an kai kararsa kotu yakamata a bashi damar kare kansa
  • Secondus ya yi zargin cewa labarin dakatar da shi ya fito ne daga ofishin na kusa da gwamnan jihar Ribas
  • Secondus da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, basu jituwa, inda Wike ya matsa lamba a tsige shugaban PDP

Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya yi martani kan hukuncin kotu na dakatar da shi daga shugabancin PDP.

Secondus yace matukar an shigar da kararsa kotu to ya kamata ace yasani kuma an bashi damar kare kansa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Shugaban ya maida wannan martani ne a wani jawabi da kakakinsa, Ike Abonyi, ya fitar ranar Litinin.

Shugaban Jam'iyyar PDP, Uche Secondus
Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Maida Martani Kan Hukuncin Kotu Na Dakatar da Shi Daga Mukaminsa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jawabin yace:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Secondus

"Idan har an kai karar Secondus da jam'iyyarsa PDP ya kamata a basu dama su kare kansu."
"Secondus da PDP ba su jin tsoron shiga kotu, wannan jam'iyya tana da tarihi, kuma ta mutane ce, ta fi karfin wani mutum ko kungiya su juya akalarta."

Wannan shiryayyen abu ne daga Ribas

Akonyi ya yi ikirarin cewa an kirkiri labarin umarnin dakatarwar ne ta ofishin mai baiwa gwamnan Ribas shawara ta musamman kan watsa labarai.

Sai dai rahoton Legit.ng Hausa ya nuna cewa mai shari'a Gbasam, shine ya bada umarnin dakatarwar yayin da yake yanke hukunci kan karar da aka shigar mai lamba PHC/2183/CS/2021.

An bayyana shugaban PDP, Secondus da jam'iyyarsa ta PDP a matsayin waɗanda ake kara na ɗaya da na biyu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Mambobin NWC 7 sun yi murabus

Yayin da ake cigaba da kiran shugaban PDP ya yi murabus, mutum 7 daga cikin mambobin kwamitin zartarwa sun mika takardar murabus ranar 3 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Shugaban Afghanistan ya tsere da makudan kudade cike da jirgi da motoci

Waɗanda suka ɗauki wannan mataki sun zargi shugaban PDP da rashin adalci da kuma watsar da su a shugabancinsa, zargin da ya musanta.

A wani labarin kuma Hisbah ta garkame Jarumar Kannywood kan saka al'amuran baɗala a kafar sada zumunta

Hukumar Hisbah ta kulle jarumar masana'antar shirya fina-finai Kannywood, Sadiya Haruna, bisa saka abubuwan baɗala a shafukanta na sada zumunta.

Dailytrust ta ruwaito cewa shugaban sashin kula na hukumar Hisbah, Malam Aliyu Usman, shine ya jagoranci damke wacca ake zargi, mazauniyar Kabuga a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel