Hotunan budurwa mai shekaru 28 da wata yarinya mai shekaru 17 ta kashe a Kano

Hotunan budurwa mai shekaru 28 da wata yarinya mai shekaru 17 ta kashe a Kano

  • A ranar 19 ga watan Augustan 2021 ne wani mummunan lamari ya faru a karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano
  • Wata Aisha Kabiru mai shekaru 17 ta sharba wa wata Bahijja Abubakar wuka wanda hakan ne sanadiyyar rasa ranta
  • Sai dai wacce ake zargin ta bayyana cewa wata hayaniya ce ta barke tsakaninsu kasancewarsu makwabta

Kumbotso, Kano - A ranar Alhamis 19 ga watan Augusta ne wata Aisha Kabiru mai shekaru 17 ta sharbawa makwabciyar ta, Bahijja Abubakar mai shekaru 28 wuka wanda hakan ne yayi sanadiyyar rasa ranta.

LIB ta ruwaito yadda mummunan lamarin ya faru a Shekar Maidaki Quaters dake karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano.

Hotunan matashiya mai shekaru 28 da yarinya mai shekaru 17 ta sheke har lahira a Kano
Aisha, yarinya mai shekaru 17 da ta sokawa budurwa wuka a wuya. Hoto daga Khadijamara Adam
Asali: Facebook

Wacce ake zargin ta amsa laifinta inda tace sun samu wata hayaniya ne da mamaciyar hakan ya janyo barkewar dambe a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'

Bayan an sasanta su ne daga baya ta dauki wuka mai kaifin gaske ta lallaba ta sharbawa Bahijja a wuyanta wanda ya kaiga ajalinta daga nan ta boye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana yadda lamarin ya faru, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Kakakin hukumar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wata takarda da ya saki a ranar Asabar, 21 ga watan Augusta ya ce Aisha ta sharba wa Bahijja wuka a wuya ta baya, inda tabar ta cikin jini.

Kamar yadda takardar tazo:

A ranar 19/08/2021 da misalin karfe 11pm muka samu rahoton yadda wata ta sharbawa Bahijja Abubakar mai shekaru 28 wuka a wuyanta ta tsere ta bart a cikin jini duk a Shekar Maidaki Quarters dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, a cewarsa.
Bayan samun wannan rahoton ne kwamishinan ‘yan sanda, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayar da umarni, inda yace SP Mudassir Ibrahim, DPO na yankin Kumbotso ya kai dauki.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata

Hotunan matashiya mai shekaru 28 da yarinya mai shekaru 17 ta sheke har lahira a Kano
Gawar Bahijja Abubakar bayan an gama sallatarta, za a kai ta makwanci. Hoto daga Khadijamara Adam
Asali: Facebook
Bayan isar ‘yan sandan ne suke zarce Asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake Kano inda aka kwanta da ita. Sai dai washe gari da safe ta amsa kiran mahaliccinta a asibitin.
An kama Aisha Kabiru, mai shekaru 17 ‘yan anguwarsu mamaciyar da misalin karfe 10 na safe a Zawaciki Quarters dake karamar hukumar Kumbotso a inda ta boye.
Bayan ta sha tambayoyi da tsananin bincike, ta amsa laifinta inda tace dambe ne ya barke tsakaninsu amma bayan an shiryasu ta koma ta sharba mata wuka a wuya wanda hakan ne ya zama ajalinta.
Kwamishinan ‘yan sandan Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayar da umarnin a mayar da lamarin ga bangaren binciken masu laifi na musamman don cigaba da zurfafa bincike.

'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara

A wani labari na daban, yan bindiga sun kashe mutane hudu sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen 50 a garin Gora Namaye da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara kamar yadda yan sanda suka sanar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wani mutum da bindigogi 53 a jihar Nasarawa

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in hulda da mutane na rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Litinin a Gusau.

Shehu ya ce maharan, sun zo da dimbin yawa sun kutsa garin da tsakar daren ranar Lahadi, suka kashe mutane hudu sannan suka sace mutane 50, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: