Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara

  • Yan bindiga sun afka garin Goron Namaye sun kashe mutum hudu sun sace 50 a Zamfara
  • Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bakin kakakinta SP Muhammad Shehu ta tabbatar da hakan
  • Kakakin yan sandan ya ce kwamishinan yan sanda ya tura jami'ai domin ceto wadanda aka sace tare da tabbatar da doka da oda

Jihar Zamfara - Yan bindiga sun kashe mutane hudu sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen 50 a garin Gora Namaye da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara kamar yadda yan sanda suka sanar a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in hulda da mutane na rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Litinin a Gusau.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Shehu ya ce maharan, sun zo da dimbin yawa sun kutsa garin da tsakar daren ranar Lahadi, suka kashe mutane hudu sannan suka sace mutane 50, The Cable ta ruwaito.

Wane mataki rundunar yan sanda ta dauka?

Kazalika, ya ce an tura jami'an yan sanda na musamman zuwa yankin a halin yanzu.

A cewarsa, Kwamishinan yan sandan jihar, Yakubu Elkana, ya bada umurnin a fara aikin ceto wadanda aka sace nan take.

Kakakin rundunar yan sandan ya ce kwamishinan ya bukaci mutanen yankin su kwantar da hankulansu a yayin da rundunar ke aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda a garin.

Harin na Goran Namaye shine na uku da aka kai a Zamfara cikin makon da ta gabata.

A ranar 15 ga watan Agusta, yan bindiga sun sace wasu malamai da dalibai a kwallejin noma da kiwon dabobi da ke karamar hukumar Bakura na jihar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

An kashe dan sanda da wasu faran hula yayin harin.

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel