Da dumi-dumi: An kama wani mutum da bindigogi 53 a jihar Nasarawa

Da dumi-dumi: An kama wani mutum da bindigogi 53 a jihar Nasarawa

  • 'Yan sanda sun cafke wani matashi a lokacin da yake safarar bindigogi kirar AK-47 guda 53 a Jihar Nasarawa
  • Har ila yau, an kuma gano albarusai akalla guda 260 a wurin mutumin da ya shiga hannu a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta
  • Matashin ya shiga hannu ne a hanyarsa ta safarar makaman zuwa wani wuri da ba a sani ba

Nasarawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wani mutum mai suna Likita Abubakar da makamai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an cafke Likita mai shekara 35 dauke da bindigogi 53 kirar AK-47 da harsasai 260, a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.

Da dumi-dumi: An kama wani mutum da bindigogi 53 a jihar Nasarawa
'Yan sanda sun kama wani mutum da bindigogi 53 a jihar Nasarawa Hoto: SH
Asali: Facebook

An tattaro cewa yana shirin kai makaman zuwa wani waje da ba a sani ba a cikin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya shaida wa Aminiya cewa an cafke wanda ake zargin ne a karamar hukumar Akwanga da ke jihar.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin Najeriya ta damke mai yi wa Boko Haram safarar taki a Yobe

'Yan sanda a Katsina sun damke mai baiwa 'yan bindiga bayanan sirri

A wani labarin, hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta damki wani mutum mai shekaru 40 wanda ake zargin mai baiwa masu garkuwa da mutane bayanai a karamar hukumar Faskari dake jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin hukumar, SP Gambo Isah ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a Katsina.

A cewarsa hukumar ta kama wani tsohon mai laifi wanda yayi karyar jami’in NCS ne yayin da yake satar babur, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel