Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'

Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'

  • Bayan barkewar rikici tsakanin jaruman Kannywood guda biyu, Ummi Rahab da Adam Zango wata barazana ta biyo baya
  • Jarumar wacce kowa ya san ta da uban gidan na ta, ta yi barazanar tona masa asiri matsawar bai daina bata mata suna ba
  • Barazanar ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani inda wasu suke cewa akwai alamar tambaya a kan lamarin

Kano - Fitacciyar jarumar kannywood Ummi Rahab, wacce ta yi fice saboda Ubangidanta, Adam Zango bayan kacamewar wani rikici tsakaninsu ta magantu.

Kamar yadda mujallar fim ta wallafa, jarumar ta yi wa Zango kashedi inda tace matsawar ya cigaba da yada maganganu na batanci a kanta, za ta fallasa asirinsa.

Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'
Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'. Hoto daga @official_adam_zango da @ummi_rahab
Asali: Instagram

Barazanar ta janyo cece-kuce

Barazanar da ta janyo mata zage-zage da munanan kalamai daga masoyan Adam Zango.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan mutane sun kula da yadda jarumin ya cire ta daga wani fim dinsa mai dogon Zango, 'Farin Wata Sha Kallo' wanda aka dade ana nunawa a Youtube, alamun tambayoyi iri-iri suka bayyana.

Wasu sun yi hasashen cewa sun samu sabani, ashe kuwa hakan ne. Don sabanin na su har ya janyo rarrabuwar kawunan magoya bayansu don yanzu haka kamfanin Northeast Records wanda na Lilin Baba ne ya rungumi jarumar.

Yanzu haka ta fara fitowa fim din tare da manyan jarumai kamar Ali Nuhu, Abdul M Shareef da sauransu.

Dalilin haka wasu suke gani kamar an zuga ta ne ta yi habaici ga tsohon ubangidan na ta har da barazana.

Kamar yadda Ummi Rahab ta wallafa a shafinta na Instagram, ta ce:

Na ji ka na fadin wai ka na so ka yi min tarbiyya amma na bijire maka. Idan har ka ci gaba da neman bata min suna ta wannan sharrin, wallahi sai na tona maka asiri.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

A karkashin wannan wallafar ne ta kara da cewa,:

Idan kunne ya ji....?

Duk da dai bata bayyana sunansa ba a wallafar da ta yi, amma kowa ya fahimci cewa da shi take sakamakon yadda kowa ya san wainar da ake toyawa.

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

A wani labari na daban, ministan kula da harkokin 'yan sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi, Ministan shari'a, Abubakar Malami da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, suna daga cikin jiga-jigan da suka halarci bikin auren 'ya'ya 10 na Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a ranar Lahadi.

Daily Trust ta tattaro cewa ministocin sun wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a wurin bikin.

Sauran jiga-jigan da suka halarci bikin sun hada da tsoffin Gwamnonin Sokoto da Zamfara, Yahaya Abdulkareem da Abdulazeez Yari, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahya Abdullahi wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal da sauran 'yan majalisu.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Asali: Legit.ng

Online view pixel