Jarumar Kannywood ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata

Jarumar Kannywood ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata

  • Wata jarumar masana'antar shirya fina-finai na Kannywood ta yi barazanar tona asirin wasu manyan jam'ian Hisbah
  • A cikin wani bidiyo, ta yi ikrarin cewa, akwai wadanda ke neman mata daga cikin jaam'ian Hisbah
  • Ta bayyana haka yayin da take bayyana fushinta kan yadda hukumar Hisbah ta kame wata Sadiya Haruna

Kano - Shahararriyar jarumar Kannywood, Umma Shehu, ta yi barazanar tona asirin jami’an hukumar Hisba ta jihar Kano wadanda ta yi zargin suna neme-nemen mata.

Umma ta bayyana haka ne cikin wani faifan Bidoyo da ya shahara a kafafen sada zumunta, inda take jimamin yadda 'yan Hisbah suka kame wata kawarta, Sadiya Haruna bisa laifin shirya bidiyon batsa.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar Hisbah ta kamewa tare da sanar da gurfanar da wata shahararriya kafafen sada zumunta, wacce aka zarga da yin bidiyon batsa, kuma Hisbah ta ce ya saba doka.

A ikrarin Umma Shehu, Hisbah ba ta da hurumin kame Sadiya Haruna, kasancewar laifi ne wanda idan ma ta aikata tsakanin ta da ubangijinta ne, kuma a cewarta, zai iya yafe mata ya kuma shirye ta.

Ta kuma yi zargin cewa, hukumar Hisbah din ta kasance mai katsalandan kan abubuwan da basu shafe ta ba, wanda a cewar Umma Shehu, ya kamata su yi abin da ke gabansu ai kowa ma yana nasa laifi.

Jarumar Kannywood ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata
Umma Shehu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A bangare guda, Umma ta yaba wa gwamnatin Malam Nasir ElRufai, inda ta ce a garin, gwamnan bai da wata matsala ta sanya wa mutane ido, hasalima, abin da yake a doka shi gwamnan yake bi.

A cikin 'yan Hisbah akwai masu neman mata

A ikrarin ta cikin bacin rai, Umma ta yi baranazar ambatan sunan wasu jami'an hukumar ta Hisbah, inda ta bayyana cewa, a cikinsu akwai wadanda su ma 'yan neman matan banza ne.

A cikin bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a Facebook, an ga Umma Shehu tare da wata kawarta a cikin mota, ta kuma bayyana bacin ranta game da batun.

A cewarta:

"Ko 'yan Hibah ne idan nace zan kira suna za a ji ba dadi, akwai masu neman matan su ma. Wallahi! Wallahi!! idan ka ce za ka kira suna sai an yi mamaki. 'Yan Hisbah, kuma manyansu..."

Haramun ne: Wani dalibi ya gina gunkin Aisha Yesufu, aikinsa ya jawo cece-kuce

A wani labarin, Wani matashi dalibi dan Najeriya mai suna Omoregie Emmanuel ya gina gunkin 'yar gwagwarmaya kuma 'yar kasuwa Aisha Yesufu.

Dandalin Just Event Online ta ba da rahoton cewa Omoregie ya gina gunkin a matsayin wani bangare na ayyukansa don kammala karatun digiri a fannin fasahar zane-zane na 'Fine and Applied Arts'.

Saurayin ya zabi ya gina gunkin A'isha ne domin yaba mata bisa gwagwarmayar da ta yi a 'yan kwanakin nan. Omoregie ya kaddamar da aikin gunkin a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta.

A cikin hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta, gunkin ya nuna shahararren hoton Aisha yayin da take daga tutar Najeriya a sama.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel